Za a ci tarar dirhami 500 kan shan karan taba a Hadaddiyar Daular Larabawa

Baya ga barazanar cutar da lafiya da taba ke yi wa masu zukarta, Gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa na shirin tura jami’an leken asiri, don gano masu shan taba a wuraren da aka hana.Duk wanda aka kama yana shan karan taba, to doka ta tanadi hukuncin tarar Dirhami 500Wani sakataren hukumar lafiya da ya gana jaridar […]

Za a ci tarar dirhami 500 kan shan karan taba a Hadaddiyar Daular Larabawa
Za a ci tarar dirhami 500 kan shan karan taba a Hadaddiyar Daular Larabawa

Baya ga barazanar cutar da lafiya da taba ke yi wa masu zukarta, Gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa na shirin tura jami’an leken asiri, don gano masu shan taba a wuraren da aka hana.
Duk wanda aka kama yana shan karan taba, to doka ta tanadi hukuncin tarar Dirhami 500
Wani sakataren hukumar lafiya da ya gana jaridar Khaleeejtimes, ya bayyana cewa, aiwatyar da dokar hana shan taba da gwamnatin tarayya ta fara ne a matakin farko. Al’amarin ya biyo bayan kafuwar dokar tun a shekarar 2014, kodayake gwamnati ba ta tsananta ba, wajen aiwatar da dokar tun farko.
– Zukar karan taba a cikin mota da yara ke ciki, wadanda shekarun su ba su kai 12 ba, zai haifar wa mutum tarar Dirhami 500. – shan tabar bututu ta Shisha a bainar jama’a za ta jawo wa kmutum tarar dirhami 500.
– Tarar shan taba ta kama daga Dirhami dubu 100 zuwa miliyan daya a kn duk wanda ya saba wa dokar hana shan taba ko tallarta.
–  Har ila yau, wannan doka cin tarar Dirhami 500 za ta hau kan direbobin da suka jefar da guntuwar taba tat agar mota. Sannan akwai tarar da ta kama daga Dirhami 500 zuwa dubu 10 kan duk wanda aka samu yana sayar da taba ga kananan yaran da shekarun sub a su kai 18 ba. Shi ma wanda ya jefar da guntuwar taba a jkan hany ko bainar jama’a akwai tarar Dirhamio 500. Wanda aka samu ya shigo da taba ko fasakwaurinta sabanin dokokin Hadaddiyar Dular Larabawa, tararsa/ta ta kama daga dirhami dubu 100 zuwa miliyan guda.
Bayan ga wannan tarin tara, akwai wadansu hukunce-hukuncen da doka ta tanada, kamar haka:
An hana zukar karan taba a bainar jama’a da motocin sufuri da jama’a ke shiga. Sannan sai mutum ya nemi izinin shan taba a kantunan sayar da kayan kawa, ko wurare na musamman da aka kebe don zukar tabar bututu ta shisha. Kuma dokar hana shan taba ga wadanda shekarun sub a su kai 18 ba, a birnin Dubai shekarun sun kama daga 20 mne. An haramta kafa katunan zukar tabar Shisha a rukunin unguwannin da jama’a ke zaune. Akwai bukatar wuraren zukar tabar bututu ta Shisha su kasance mita 150 daga wurin ibada, koi cibiyoyin ilimi. An hana tallar taba ko nau’ukanta a bainar jama’a. Akwai daurin shekara biyu ga duk wanda ya shigo da tabar da ba ta dauke da wani gargadi game da illolinta ba. Ba a amince da shan taba ba, a  gidan sayar da abinci, wanda fadin sa da tsawonsa bai wuce kafa dubu ba. Ya zama dole a yi zane da rubutaccen gargadi a kwalin sigari.