Za a cire mutum-mutumin Messi saboda barazanar tsaro a Indiya

Mutum-mutumin ya nuna tauraron ɗan wasan Argentina yana ɗaga Kofin Duniya da ya lashe tare da ƙasarsa.

Za a cire mutum-mutumin Messi saboda barazanar tsaro a Indiya

Mahukunta a Jihar West Bengal da ke ƙasar Indiya sun sanar da shirin cire wani katafaren mutum-mutumin tauraron ƙwallon ƙafa Lionel Messi da aka gina a birnin Kolkata, bayan injiniyoyi sun gano cewa yana girgiɗi a duk lokacin da iska ke kaɗawa.

An gina mutum-mutumin mai tsawon mita 21, wanda aka yi da launin zinariya, domin tunawa da ziyarar da Messi ya kai Indiya a watan Disamban bara.

Mutum-mutumin ya nuna tauraron ɗan wasan Argentina da Inter Miami yana ɗaga Kofin Duniya da ya lashe tare da ƙasarsa.

Sai dai wani ɗan majalisar Jihar West Bengal, Sharadwat Mukherjee, ya bayyana cewa binciken da injiniyoyin gwamnati suka gudanar ya nuna cewa mutum-mutumin ba shi da cikakken aminci.

Ya ce jami’ai sun lura cewa mutum-mutumin na girgiɗi da motsi idan iska ta taso, lamarin da ya jawo fargabar cewa zai iya zama barazana ga rayukan jama’a, musamman ganin yadda aka kafa shi a kusa da wata babbar hanya mai cunkoson ababen hawa.

A ranar Laraba, an hangi ma’aikata suna hawa saman mutum-mutumin tare da ɗaura igiyoyi a jikinsa domin ƙoƙarin daidaita shi kafin a cire shi gaba ɗaya.

Mukherjee ya ce har yanzu ba a tantance ranar da za a sauke mutum-mutumin ba, yana mai cewa aikin cire shi ya fi yadda aka zata wahala.

Ya kuma ce ba a yanke hukunci ba kan ko za a sake kafa mutum-mutumin a wani wuri daban ko akasin haka.

Messi mai shekara 38 na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin fitattun ‘yan wasan ƙwallon ƙafa a duniya, kuma ana sa ran zai jagoranci Argentina wajen kare kambunta a gasar cin kofin duniya mai zuwa.

Ko da yake Messi bai fito fili ya tabbatar da cewa zai buga gasar ba, rahotanni na nuna cewa ana tsammanin zai haska a gasar, wanda hakan zai sa ya kafa tarihin bayyana a gasar cin kofin duniya sau shida.

Indiya dai ƙasa ce da aka fi saninta da wasan cricket, amma ƙwallon ƙafa na ci gaba da samun karɓuwa sosai a tsakanin al’umma, inda wani bincike da kamfanin Nielsen ya fitar ya nuna cewa ƙwallon ƙafa ce ta biyu mafi shahara a ƙasar bayan cricket.