Za a ciyar da daliban firamare da kudin da aka kwato daga barayin gwamnati – Sanata Gumel

Yayin da Majalisar Dokoki ta kasa ta rattaba hannu kan kasafin kudin bana, nan ba dadewa ba Gwamnatin Tarayya za ta fara ciyar da daliban makarantun firamare a daukacin kasar nan ta hanyar amfani da kudin da aka kwato daga barayin gwamnati.A nasa ran daliban firamare miliyan biyar da rabi ne za su ci moriyar […]

Za a ciyar da daliban firamare da kudin da aka kwato daga barayin gwamnati – Sanata Gumel
Za a ciyar da daliban firamare da kudin da aka kwato daga barayin gwamnati – Sanata Gumel

Yayin da Majalisar Dokoki ta kasa ta rattaba hannu kan kasafin kudin bana, nan ba dadewa ba Gwamnatin Tarayya za ta fara ciyar da daliban makarantun firamare a daukacin kasar nan ta hanyar amfani da kudin da aka kwato daga barayin gwamnati.
A nasa ran daliban firamare miliyan biyar da rabi ne za su ci moriyar tallafin ciyarwar a fadin kasar nan kamar yadda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta tabbatar.
Sanata Abdullahi Abubakar Gumel da ke wakiltar Jigawa ta Arewa ne ya fadi haka a wata hira da ya yi da manema labarai a wajen daurin auren ’yar Gwamnan Jihar Jigawa a ranar Asabar da ta gabata a Masallacin Aliyu bn Abu Talib da ke birnin Kano.
Sanata Abdullahi Gumel ya kara da cewa ciyarwar ta kwanaki 200 a shekara saboda cire ranakun
Asabar da Lahadi, kowane dalibi Gwamnatin Tarayyar za ta rika kashe masa Naira 70 a kowace rana.
Ya ce a tsawon kwanakin 200 gwamnati za ta kashe wa daliban makarantun firamare Naira biliyan 77 a kokarinta na bunkasa ilimi a kasar nan.
Sanata Abdullahi Gumel ya ce wadannan kudi suna daga cikin kudaden da Gwamnatin Tarayya ta amso daga wajen wadansu shugabanni da suka wawure a zamanin gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan, inda aka kwato kimanin Naira biliyan 500.
Sanata Gumel ya ce Gwamnatin Tarayya za ta kuma dauki malaman da za su rika koyarwa a makarantun firamare da makarantun sakandaren hada-ka dubu 500 a kokarin gwamnatin na habaka ilimi a Najeriya, inda ya ce dukkan malaman da za a dauka za su rika samun albashin da bai gaza Naira dubu 25 ba, inda albashin nasu zai cinye Naira biliyan 138 duk shekara.
Ya ce Gwamnatin Tarayya za ta bullo da wani shiri na kula da rayuwar mata da kananan yara ta hanyar tallafa wa mata kimanin miliyan daya inda kowace mace za a ba ta tallafin Naira dubu 40, domin ta samu damar dogaro da kanta yayin da mutum dubu 460, za su samu tallafin Naira dubu 200, domin su bunkasa sana’o’insu na hannu.
Sanatan ya ce kafin a ba da tallafin dole sai an yi rajistar sunayen jama’a a cikin na’urar kwamfuta tare da daukar hoton yatsunsu domin kauce wa magudi ko tauye wasu.
Da ya juya kan bunkasa aikin gona Sanata Abdullahi Gumel ya ce Gwamnatin Tarayya za ta bai wa manoma tallafin bashin noma na Naira dubu 200, domin sayen garma da shanun noma, yayin da gwamnatin za ta bai wa malaman gona masu bai wa manoma shawara Naira dubu 100 domin inganta harkar noma a yankunan karkara da birane.
Sanatan ya ce gwamnati za ta aiwatar da shirin tallafa wa marasa galihu da nakasassu da alawus din Naira dubu biyar-biyar a wata, inda za a fara shirin da nakasassu kamar miliyan daya a  bana.