Za a daga darajar filin jirgin Ibadan don jigilar alhazai

Gwamna Seyi Makinde ya yi alkawarin kammala aikin cikin watanni 18 masu zuwa

Za a daga darajar filin jirgin Ibadan don jigilar alhazai

Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ya yi alkawarin kammala aikin daukaka darajar filin jirgin sama na Ibadan domin fara jigilar maniyyata aikin Hajji daga nan.

Makinde ya ba da tabbacin kammala aikin daga darajar filin jirgin cikin watanni 18 masu zuwa.

Ya yi wa al’ummar Musulmi wannan alkawari ne a ranar Laraba a wajen liyafar Sabuwar Shekarar Musulunci Hijira ta 1446 a gidan Gwamnati dake Agodi a Ibadan babban birnin Jihar Oyo.

Gwamnan ya bugi kirjin cewa gwamnatin jihar tana da wadataccen kudi da dukkan abubuwan gudanar da wannan aiki na daukaka darajar filin jirgin.

Ya ce kafin karshen makon da muke ciki zai kafa kwamitin da za a damka wa alhakin lura da wannan muhimmin aiki.

Gwamna Seyi Makinde ya yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga al’ummar jihar su sa ido wajen yin maraba da sabuwar Jihar Oyo da ba a samu irinta a baya ba.

A cewarsa, Sabuwar Jihar Oyo za ta haifar da kauna da son juna da hadin kan jama’a ba tare da bambancin addini ko kabila ba, da kuma zaman lafiya mai dorewa a jihar.

Ya ce yana sane cewa akwai kalubale masu yawa da suke fuskantar jihar da kasa baki daya, don haka ya yi fatan shawo kan matsalolin da hadin kan jama’a da goyon bayansu.

Dangane da taron liyafar da Gwamnatin sa ta dauki nauyin shiryawa, sai ya kada baki ya ce, “mun riga mun bayar da hutun Sabuwar Shekarar Musulunci ta bana.

“A yau kuma mun shirya liyafar murnar zagayowar shekara hijira ta 1446 ne.

“Muna rokon za ku goyi bayan gwamnati a kan shirye-shiryenta na cigaban Jihar.”

Sheikh Najimudeen Alkubroh wanda ya gabatar da lacca a wajen taron ya jinjina wa Gwamna Seyi Makinde a kan sabon salon mulkin da ya bullo da shi a jihar da ake matukar bukatar irinsa a kasa baki daya.

Shi kuwa Cif Bayo Oyero da ya shugabanci taron, kira ya yi ga malaman Musulunci su kasance a kowane lokaci cikin bibiyar kwanan watan Kalandar Musulunci da koyar da mabiya muhimmancinsa.

A cikin jawabansu, Farfesa Kamil Oloso da Farfesa Musliudeen Yahya da Sanata Monsurat Sunmonu sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta rika bayar da hutun Sabuwar Shekarar Musulunci.

Sarkin Musulmi na Kasar Yarbawa, Alhaji Dawud Makanjuola Akinola da Babban Limamin Ibadan, Sheikh Abubakar Agbotomokekere, su ne suka jagoranci manyan limamai da malamai da jiga-jigan Musulmi na Jihar Oyo zuwa wajen taron.

Shekararu da tawagarsa sun yi watsi da tsarin rabon haraji

An lalata turakun wuta 18 cikin kwanaki 5 a Najeriya — TCN

Sibil Difens ta kama mutum 10 kan aikata laifuka daban-daban a Gombe

’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6 a Gombe