Za a daina zaman kurkuku a Saudiyya

Hukumar Shari’a ta Saudiyyata umarci kananan kotunan kasar da su fara aiwatar da tsarin da zai maye makwafin zaman kurkuku, ta yadda za a ria sanya mai laifin ayyukan ddasuka hada da kula da tsofaffi ko hakar kabarui da wankin gawa da sauramn ayyukan aka tsara aiwatarta don rage cunkoson gidajen yari. A wata takardar […]

Za a daina zaman kurkuku a Saudiyya
Za a daina zaman kurkuku a Saudiyya

Hukumar Shari’a ta Saudiyyata umarci kananan kotunan kasar da su fara aiwatar da tsarin da zai maye makwafin zaman kurkuku, ta yadda za a ria sanya mai laifin ayyukan ddasuka hada da kula da tsofaffi ko hakar kabarui da wankin gawa da sauramn ayyukan aka tsara aiwatarta don rage cunkoson gidajen yari.

A wata takardar umarni da hukumar shari’ar ta aike wa kotunan, wadda ta yi walakabin dabarazr maye makwafin zaman kurkuku,l na daga cikin matakan da aka yanke matsaya a kansu, a wani bincike da ma’aikatar harkokin cikin gida ta gudanar, kan yadda za a shawo kan aikata miyagubn laifuka da suka hada da “sava wa iyaye,” al’amuran da aka tattauna a kansu a taruka kara wa juna sani.
Ayyukan da za a rika sanya mai laifi, maimakon zaman kaso, sun hada da aiki a gidan gajiyayyu ko tsofaffi tukuf da wankin gawa da haka kaburbura da hidima a cibiyoyin gyara halinka, kamar yadda jaridar kullum ta Al –Watan ta ruwaito, a ranar Alhamis din makon jiya.
Hukumar shari’ar ta jadadda muhimmacin aiwatar da wadannan tsarer-tsare, a maimakon zaman kurkuku don a rage yawan wadanda ke tsare a gidajen yarin kasar.
Wani marubuci da ya lakaba wa kansa sunan Zainak, ya nuna goyon bayansa kan a rika sanya mai laifi ayyukan da suka shafi janaza da haka kaburbura, inda ya nuna cewa wannan mataki da akadauka ya dace.
“Wannan zai sanya zukatansu su yi laushi a lokacin da suke ganin mutuwa a kusa da su,”kamar yadda Zainak ya rubuta. “Wannan zai sanyasutuba, su zamamutanen kirki masu biyayya ga iyaye, ta yadda za su8 rikakyautata musu,” kamar yadda yake kunshe a makalarsa.
A farkon wannan shekarar ne, aka bayar da rahotannin yadda Ma’aikatar Shari’a ke aikin kan sabon tsarin yanke hukunci, wanda zai fara aiki nan da Disambar bana. Wannan doka ita ce tsarin da ake so alkalai su rika amfani da ita, wajen yanke hukunci ga masu laifin dake wajen gidan yari, ta yadda za su rika yin aikin hidima gaal’umma, musammam ma a kokarin da ake yi wajen rage cunkoson gidajen kurkuku da kashi 50 cikin 100.
A cewar rahotannin, wannan sabon tsarin hukuncin da ake amfani da shia yanzu, an baiwa alkalai wuka da nama su yi gaban kansu.