Za a dasa kyamarori domin hana satar jarrabawa a China
Za a haramta wa dalibai sanya kaya masu karafa da suka hada da bel da agogo.
Kasar China na kokarin samar da wani tsarin sanya ido domin hana magudi a jarrabawar shiga jami’a.
Biranen kasar da dama na shirin kafa tsare-tsaren sa ido domin hana magudi, yayin da dalibai kusan miliyan goma sha uku ke shirin yin jarrabawar shiga jami’a ta bana.
- An dauke wa kamfanonin da ke kera motoci masu lantarki harajin shekara 10
- Farashin gas din girki da man jirgin sama ya karye
Za a samar da na’urorin tantance fuska domin hana sojojin haya da ke karbar kudi domin su zauna wa wasu jarabawar na kwanaki uku.
Har ila yau, za a haramta wa dalibai sanya kaya masu karafa da suka hada da bel da agogo, don rage yiwuwar wasu daliban su yi amfani da kyamarori da na’urorin saurare a zauren jarrabawan.
A shekarar 2020, an yanke wa wani dalibi hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari bayan ya yi amfani da na’urar sadarwa ta sirri don samun taimako wajen amsa tambayoyin jarrabawa.