Za a dasa wa yaron da aka kwakule wa ido idanun roba

Babban likitan ido da ke asibitin koyarwa ta Jami’ar Ahamdu Bello da ke Shika Zariya da ya jagoranci yi wa Abubakar Usman yaron da aka kwakule masa idanu a Zariya aikin tiyatar ido Dokta Chida ya ce za su dasa wa yaron idanun roba. Sai kuma Dokta Chida ya bayyana cewa ‘’a sakomakon amfani da karfi […]

Za a dasa wa yaron da aka kwakule wa ido idanun roba
Za a dasa wa yaron da aka kwakule wa ido idanun roba

Babban likitan ido da ke asibitin koyarwa ta Jami’ar Ahamdu Bello da ke Shika Zariya da ya jagoranci yi wa Abubakar Usman yaron da aka kwakule masa idanu a Zariya aikin tiyatar ido Dokta Chida ya ce za su dasa wa yaron idanun roba.
 Sai kuma Dokta Chida ya bayyana cewa ‘’a sakomakon amfani da karfi da aka yi wurin kwakule idanun ya janyo lalacewar mazaunin idanunsa da kuma tsinkewar jijiyoyin da ke sanya sa gani na idon, wanda a sakomakon hakan yaron ba zai sake gani ba, sai dai kawai yanzu za mu sanya masa idanun roba domin cike kwarmin idon.’’
 Likitan ya kara da cewa, ‘za mu yi kokarin mu samo idanun roba wadanda za su yi daidai da kwarmin idonsa domin mu sa masa, amma ba don ya gani da su ba sai dai kawai don mu gyara fuskar ta yi kyau, kuma yanzu haka duk mun gyaggyara abubuwan da ya kamata mu gyara masa, kuma yana samun sauki. Idan muka dasa masa wadannan idanun, nan gaba kuma bayan kamar shekara biyu zai zo mu cire wadannan da za mu dasa masa yanzu mu sa masa na daidai da wannan lokacin, domin kodayaushe fuskar na kara girma ne, amma a yanzu ba zai sake gani ba.’’
Dokta Chida ya bayyana cewa aikin bai da wahala, ‘’sai dai kawai yanayin kula da shi idan an sanya wa wanda duk aka sanya masa, ka ga kamar na wannan yaron tun yaro ne zai rika zuwa bayan lokaci-lokaci ana sake masa wani wanda zai yi daidai da kwarmin idonsa, kuma ba shi da wani tsada, tun da idanunsa ba za su sake gani ba, sai dai kawai don ado.’’   
Da Aminiya ta tutubi  mahaifin yaron mai suna Malam Usman Isa Auta domin jin ko ya gamsu da irin kokarin da ake yi wajen ceto idanun yaron? Sai ya ce, “kwarai da gaske, domin daga lokacin da abun ya faru har zuwa yau ba mu yi amfani da ko sisi na,mu ba na farko Mai martaba Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris shi ya dauki nauyin yaron inda ya tura mu babban asibitin ido na Kaduna, daga can su kuma suka dawo da mu asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya,  inda su kuma suka cigaba da kula da mu. Suna iyakar kokarinsu wajen ba mu kula sosai, kuma mutane mabanbata sun ba mu gudunmawa. Mai girma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya aiko da wakilai don su tausaya mana su kuma jajanta mana tare da ba mu kudi Naira dubu dari da hamsin da kuma dalar Amurka dari, wanda da aka canza  ta ta bamu kudin Najeriya Naira dubu talatin, tare da alkawarin daukar nauyin karatun yaron tun daga firamare har zuwa jami’a, idan Allah Ya sa ya warke. Haka kuma tsohon gwamanan jihar Kaduna Dokta Muktar Lamaran Yaro shi ma ya ziyarce mu har nan asibitin ya jajanta mana, ya kuma yi mana alheri, haka  kuma Sanata Shehu Sani,  shi ma ya ziyarce mu ya jajanta mana, haka kuma ofishin jakadancin Ingila ya turo wakilai sun duba halin da muke ciki. Don haka gaskiya muna godiya, musamman ku ‘yan jaridu kun tausaya mana kwarai kuma kun ba mu cikakken goyan baya, Allah Ya saka muku da alheri. Kuma yarona yana ta samun lafiya, ba kamar yadda ake cewa ya mutu ba.    
Da Aminiya ta tuntubi Shugaban asibitin koyarwar na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya Farfesa Khalil Muktar ya ce bai zauna da wadanda suka gudanar da aikin tiyatar ba, amman akwai matsaloli masu yawa wanda suka fi wannan duk an magance su a asibitin, don haka wannan ma ba zai gagara ba, kuma aikin dashen idon roba ba shi da wata tsada.    
Haka kuma wata kwararrar likitan idanu Amina Hassan Wali da ke aiki a Babban Asibitin Ido na kasa da ke Kaduna ita ma ta bayyana cewa za a iya dasa wa wannan yaron idanun roba amma ba zai iya gani da su ba.
A cewarta, har yanzu likitoci a kasashen duniya ba su samu nasarar gano yadda za a rika dashen idanu kamar yadda ake dashen kodar dan adam ba.
Likitar wadda ta  bayyana hakan  a tattaunawar  da ta yi da Aminiya  ta wayar tarho a Kaduna, ta bayyana cewa, “Gaskiya ba zai yiwu a dasa masa wani ido kamar yadda ake dasa koda ba. Domin har yanzu kasashen turai ba su yi nasarar fara dashen idon mutum ba. Abin da kawai za a iya yi masa shi ne a dasa masa idon roba, wanda za a saka masa amma ba zai rika gani da su ba. Ka san kafin su cire idon sai an yanke jijiyoyi da suke hade da kwakwalwar mutum, kuma da zarar sun yanke su shi ke nan babu abin da za a iya yi,” inji ta.
Game da ko akwai kwararru da za su iya saka masa idon roban a kasar nan sai ta ce, “ kwarai kuwa, ai ba sabon abu ba ne. Idanun roba dama akwai su a kasar nan kuma muna da kwararru da za su dasa masa su. Amma fa sai idan ya samu sauki, ma’ana idan ramin da aka kwakule idon ya warke sannan za a iya yi masa aiki,” inji ta.
El-Rufa’i ya yi alkawarin daukar nauyin karatunsa
Bashir Dabo Shi ne Mai bai wa gwamnan jahar Kaduna shawara a kan harkokin sadarwa ta yanar gizo, kuma yana daya daga cikin wadanda suka kai wa yaro Sadik da matsafa suka cire wa ido a birnin Zariya taimako.Ya ce hakika gwamna Malam Nasir El-Rufa’i ya tura su wajen iyayen yaron domin gane wa idonsu abin da ya faru.
“Hakika Mai girma gwamna ya yi alkawarin daukar nauyin karatun Abubakar Sadik wanda ‘yan ta’adda matsafa suka cire masa ido a Zariya, dama abin da ya fi haka, amma saboda Mai martaba Sarkin Zazzau ya fada wa Mai girma Gwamna cewa masarautar  Zazzau ta dauki nauyin  kai yaron zuwa kasar Indiya domin sama masa maganin da ya kamata.  Shi kuma sai gwamna ya ce zai duba inda ya kamata gwamnati ta shigo ciki inda ba a taba ba. In sha Allahu  idan har ya samu lafiya zai dauki nauyin karatunsa daga firemare har zuwa jami’a. Wannan shi ne alkawarin da Mai girma gwamna ya yi, ya kuma tura mu muka ziyarci iyayen yaron a karkashin jagorancin Shugaban jami’an tsaro na Operation Yaki Yakubu Soja,wanda kuma shi ne Mai bai wa gwamna Shawara a kan harkokin tsaro,  inda muka jajanta wa iyayensa a kan abin bakin cikin da ya faru da su. Daga nan ne muka dauki Naira dubu dari da hamsim muka bai wa iyayensa domin su ci abinci. Sai muka dauki Dala dari kuma muka kara masa. Sannan muka ziyarci sauran marasa lafiya  da ke asibitin.
Bashir Dabo ya kuma kara da cewa, Gwamna Nasir El-Rufa’i  ya so ya ziyarci yaron da kansa, amma saboda ba ya kasar ya tafi kasar Saudiya shi da sauraran gwamnoni a kan batun ganawa da bankin musulunci  a lokacin da abin ya faru, shi ya sa bai samu zuwa ba, sai mu aka tura su.