Za a dauki dimbin ma’aikatan jinya a Ghana

Ma’aikatar Kiwon Lafiyan kasar Ghana ta umarci duka ma’aikatun da ke karkashinta da su dauki sabbin ma’aikatan jinya da ungozoma wadanda suka kamalla samun horonsu a shekarar 2015.A wata sanarwa daga ma’aikatar kiwon lafiya ya ce nas da ungozoma, ana bukatar su karbi fom wato takadar neman aiki daga ma’aikatun kiwon lafiyar da ke kusa […]

Za a dauki dimbin ma’aikatan jinya a Ghana
Za a dauki dimbin ma’aikatan jinya a Ghana

Ma’aikatar Kiwon Lafiyan kasar Ghana ta umarci duka ma’aikatun da ke karkashinta da su dauki sabbin ma’aikatan jinya da ungozoma wadanda suka kamalla samun horonsu a shekarar 2015.
A wata sanarwa daga ma’aikatar kiwon lafiya ya ce nas da ungozoma, ana bukatar su karbi fom wato takadar neman aiki daga ma’aikatun kiwon lafiyar da ke kusa da su.
Sanarwar an yi ta ne bayan tashin jijiyoyin wuya da barazanar yin zanga-zanga da kuma tarewa a ma’aikatar har sai an biya musu bukatarsu da kungiyoyi daban-daban na nas da ungozomar ke shirin yi idan ba a saurari kokensu ba.
An dai yi amannar cewa wannan mataki da gwamnati ta dauka zai zo masu neman  aikin nas da dadi ganin cewa, hakarsu za ta cimma ruwa.
Har ila yau, ita kuma ma’aiakatar kiwon lafiya zai bunkasa mata karfin ta fannin aikin jinya.