Za a daura auren ’yar faston da ta musulunta
A yau Juma’a ne za a daura auren A’isha (Charity) Uzoechina wata daliba mai shekara 26 kuma ’yar Fasto Raymond Uzoechina da musuluntarta bara a garin Bidda da ke Jihar Neja ta jawo cece-ku-ce.Babban Daraktan kungiyar Kare Hakkin Musulmi ta Muslim Rights Concern, (MURIC), Ishak Akintola wanda kungiyarsa ce ta tsaya wa A’isha na tsawon […]

A yau Juma’a ne za a daura auren A’isha (Charity) Uzoechina wata daliba mai shekara 26 kuma ’yar Fasto Raymond Uzoechina da musuluntarta bara a garin Bidda da ke Jihar Neja ta jawo cece-ku-ce.
Babban Daraktan kungiyar Kare Hakkin Musulmi ta Muslim Rights Concern, (MURIC), Ishak Akintola wanda kungiyarsa ce ta tsaya wa A’isha na tsawon watanni ne ya bayyana haka.
Malam Akintola, wanda Farfesa ne a Jami’ar Jihar Legas ya fadi a wani sako da ya aika a shafin da MURIC ke kula da shi, inda ya ce A’isha Uzoechina za ta auri lauyan da ya tsaya mata ne a lokacin da ake takaddama kan musuluntarta.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Mista Akintola ya fadi a cikin sakon cewa: “Kun tuna ’yar uwa A’ishat? Ita ce ’yar faston na da ta musulunta a bara, kuma mahaifinta ya tayar da kayar baya a Jihar Neja. MURIC ta rika sanya ido kan halin da take ciki. To za ta yi aure a ranar Juma’a 2 ga Mayu, 2014 (yau)”
Ya kara da cewa ko kun san wanda zai kasance angonta? Shi ne Barista Tijjani, lauyan da MURIC ta sa ya kula da shari’arta a kotu.”
Sai dai ba a yi bayanin wuri da yadda shagulgulan aure za su kasance ba, kuma jaridar ta ce ba ta iya jin ta bakin A’isha Uzoechina ko angonta kan lamarin ba.
Idan za a iya tunawa A’isha wadda daliba ce a Kwalejin Kimiyya da kere-kere da ke Bidda ta karbi addinin Musulunci ne a ranar 13 ga Fabrairun 2013, lamarin da ya fusata zuriyarta, tare da jawo takaddama a tsakanin mabiya addinin Musulunci da Kiristoci a kasar nan.
Bayan ta Musulunta ne ta zabi sunan A’isha, kuma sakamakon tsoro kan rayuwarta ne ta garzaya wata Kotun Shari’ar Musulunci don ba ta kariya daga mahaifanta.
Kotun ta bukaci Etsu Nupe kuma shugaban Majalisar Sarakuna ta Jihar Neja Alhaji Yahaya Abubakar ya dauki nauyin rikonta.
Sai dai mahaifinta da kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) sun yi yunkurin kwace ta daga hannun Etsu Nupen inda suka zarge shi da sace ta da kuma tilasta mata shiga Musulunci.
Lamarin da Etsu Nupe ya musanta, ya ce A’isha ta nemi kariya a fadarsa ne domin gudun cutarwar da za ta iya fuskanta daga mahaifanta.
A’isha ma ta musanta hakan inda ta ce: “A bisa son raina na karbi Musulunci bayan na yi nazarinsa a tsanake. Na shiga Musulunci ne bisa radin kaina. Ina sha’awar dabi’un Musulmin da nake hulda da su, musamman yadda suke tafiyar da rayuwarsu. Kun san Musulmi sun yi imani da Allah,” kamar yadda ta shaida wa kafar sadarwa ta OnIslam.net a lokacin.
Ta kara da cewa: “Ina da kawaye Musulmi, kuma ina ganin abin da suke yi, wannan ne ya ja ra’ayina na karbi Musulunci.”