Za a daure duk malamin da ya yi batanci lokacin tafsiri a Kaduna … Neja za ta hukunta wanda ya tunzura jama’a

Babban Sakataren Hukumar Kula da Harkokin Addinin Musulunci ta Jihar Kaduna, Alhaji Abdulrahman Mahmoud ya ce akwai dokar da ta hana yin batanci da wa’azin da ka iya tunzura jama’a a jihar kuma duk malamin da ya karya dokar zai tafi gidan yari na shekaru biyu.Babban Sakataren ya bayyana haka ne a lokacin da Majalisar […]

Za a daure duk malamin da ya yi batanci lokacin tafsiri a Kaduna … Neja za ta hukunta wanda ya tunzura jama’a
Za a daure duk malamin da ya yi batanci lokacin tafsiri a Kaduna … Neja za ta hukunta wanda ya tunzura jama’a

Babban Sakataren Hukumar Kula da Harkokin Addinin Musulunci ta Jihar Kaduna, Alhaji Abdulrahman Mahmoud ya ce akwai dokar da ta hana yin batanci da wa’azin da ka iya tunzura jama’a a jihar kuma duk malamin da ya karya dokar zai tafi gidan yari na shekaru biyu.
Babban Sakataren ya bayyana haka ne a lokacin da Majalisar Malamai ta jihar ta kai masa ziyara a ofishinsa, inda ya ce “Wannan doka ta hana wa’azin batanci ko zagin mutane da aka kafa a shekarar 2010 ta tanadi daurin shekara biyu ko tara ga wanda ya karya ta, ko duka.”
Ya ce hukumarsa ta zauna da malaman da za su yi tafsiri bana inda suka amince su yi tafsiri ba tare da zagi ko habaici ba. “Mun amince duk malamin da ya karya wannan matsaya za a nemi ya gyara, idan ya ki, doka za ta yi aikinta,” inji shi.
Shugaban Majalisar Sheikh Babantune ya ce sun kai ziyarar ce domin neman goyon baya a kokarinsu na hada kan Musulmin jihar. Ya ce, al’ummar Musulmi na fuskantar babban kalubale a bangaren rashin tsaro kuma hadin kan Musulmi shi ne mafita daga matsalar da Musulunci ke fuskanta a kasa da duniya baki daya.
A wani labarin, gwamnatin Jihar Neja ta lashi takobin sa kafar wando daya da duk malamin da ya tunzura jama’a lokacin tafsirin watan Ramadan na bana.
Kwamishinan Al’amuran Addini Malam Shehu Haruna Kumbashi ne ya sanar da haka a ganawa da manema labarai a Minna.Ya ce, daukar matakin ya zama wajibi ganin yadda wasu daga cikin malaman ke amfani da wannan lokaci suna yin abin da ya saba wa Musulunci.
Malam Shehu Kumbashi, ya ce gwamnatin jihar za ta sa jami’an tsaron su kama duk malamin da ya taka wannan doka komai girmansa.
Imam Umar Faruk Abdullahi, Sakataren Majalisar Limaman Juma’a ta Jihar, ya ce tafsirin da malaman za su yi a watan azumin bana zai fi na bara armashi, domin a bara ma sun yi kokarin bin dokokin da aka gindaya musu.