Za A Dawo Wa Maniyyata Rarar Kuɗin Hajji —NAHCON
Farfaɗowar darajar Naira ta sa za a a dawo wa maniyyata da rarar kudin kujerar aikin Hajjin bana
Akwai yiwuwar a dawo wa maniyyata aikin Hajjin bana canjin kudadensu, a cewar Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON).
Shugaban hukumar, Jalal Ahmad Arabi, ya ce akwai yiwuwar su mayar wa maniyyata abin da ya saura a kuɗin da suka biya sakamakon farfaɗowar darajar Naira, tunda dama tashin farashin Dala Naira ne ya sa aka samu ƙarin kuɗin tafiyar.
Karyewar darajar Naira a Najeriya ya haifar da hauhawan farashin kusan komai a kasar, ciki harda kuɗin tafiya aikin Hajji.
Amma a yanzu Naira ta fara farfaɗowa, inda ’yan kasuwar canjin kuɗaɗen ƙasashen ƙetare na samun Dala ɗaya a kan Naira 980.
- NAHCON ta mayar da kuɗin Hajjin bana kusan Naira miliyan 7
- NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Kotuna Ke Yanke Hukunci Mabambanta Kan Shari’a Iri Ɗaya
Hakan na nuna akwai dawo wa maniyyata rarar da aka samu kan kudin kujerar aikin Hajji da suka biya, Naira miliyan 6.5.
Shugaban hukumar aikin hajjin, Arabi ya bayyana hakan ne a wata hirarsa da kafar labarai ta DCL da ta wallafa a shafinta na X, ranar Alhamis.
Sai dai Jalal Arabi bai bayyana lokacin da za a dawo wa maniyyatan canjin kudin ba idan ya kama, ballantana abin da za a dawo wa kowannensu.
Amma ya bada tabbacin cewa muddin yana kan kujerar shugabancin NAHCON, ba za su ci hakkin kowa ba, zai tabbatar an biya kowa abin da ya dace.
A baya dai in aka samu rarar kuɗin aikin Hajji, hukumar na bai wa alhazai ne bayan sun dawo daga sauke farali.