Za a fara ɗaukar sabbin jami’an hukumar shige da fice da na kashe gobara a Augusta
Gwamnatin ta ce za a fara ɗaukar sabbin ma’aikatan daga farkon watan Agusta.
Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za a fara ɗaukar ma’aikatan Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa da Hukumar Kashe da Gobara ta Tarayya a watan Agusta.
Sakataren Hukumar Shige da Fice, Gyaran Hali da Hukumar Kashe Gobara, Jafaru Ahmed ne, ya bayyana haka a wata sanarwa.
- Masu garkuwa sun harbi jarogan APC sun sace ’ya’yansa a Abuja
- Kotu ta tabbatar da nadin Sanusi II a matsayin Sarkin Kano
Ahmed ya bayyana cewa, za a fara neman gurbin aikin ne a ranar 15 ga watan Yuni, 2024 zuwa ƙarshen watan Satumban 2024.
Ya tabbatar da cewa za a fitar da sunayen waɗanda suka yi nasara a matakin farko, ta hanyar tuntuɓar su kafin zuwa mataki na gaba.
Ya nemi afuwa kan jinkirin fara ɗaukar ma’aikatan kamar yadda aka tsara a baya.
Jinkirin ya faru ne saboda gudanar da binciken ma’aikatan wasu hukumomin da ke ƙarƙashin babbar hukumar.
Binciken ma’aikatan ya shafi Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa, Hukumar Kashe da Gobara ta Tarayya da Hukumar Kare Farar Hula ta Najeriya.
Duk da jinkirin, Ahmed ya tabbatar da cewa duk waɗanda suka yi nasara za su samu bayanin matakai na gaba kan abin da za a yi, ta wayoyinsu ko imel ɗinsu.