Za a fara amfani da na’ura mai kayyade yawan gudu ga ababen hawa
Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa a Jihar Kano ta ce shirye-shirye sun yi nisa wajen fara amfani da na’ura mai kayyade gudun abin hawa a kasar nan.Shugaban Hukumar Mista B.O. Oyeyemi, ya bayyana haka a wajen bikin bude sabon dakin taro da ma’aikatan sa-kai na hukumar (Special Marshal) suka gina a harabar ofishin hukumar da […]
Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa a Jihar Kano ta ce shirye-shirye sun yi nisa wajen fara amfani da na’ura mai kayyade gudun abin hawa a kasar nan.
Shugaban Hukumar Mista B.O. Oyeyemi, ya bayyana haka a wajen bikin bude sabon dakin taro da ma’aikatan sa-kai na hukumar (Special Marshal) suka gina a harabar ofishin hukumar da ke Kano.
Shugaban ya ce sanya na’urar a jikin ababen hawa zai taimaka wajen rage aukuwar hadurra a kan tituna da mugun gudun da masu ababen hawa ke yi. “Idan aka sanya
wannan na’ura a jikin abin hawa za ta hana duk direba wuce iyakar da aka kayyade masa na tafiya a kan titi koda ya so yin haka. Yin amfani da wannan na’ura zai takaita yawan aukuwar hadurra a kan titunanmu,” inji shi.
Mista Oyeyemi ya kara da cewa za a fara amfani da na’urar ne a ranar 1 ga watan Yunin bana, don haka sai ya yi kira ga masu ababen hawa su tabbatar sun mallaki na’urar kafin lokacin kasancewar hukumar ba za ta kara lokaci bayan cikar wa’adin ba.
Da yake jawabi game da dakin taron da aka bude, shugaban ya ce abu ne da ya dace wanda ya kamata sauran ofisoshin da ke kasar nan su yi koyi da su.