Za a fara amfani da takardun kudin Najeriya a Birtaniya
Mahukunta a kasar Birtaniya sun ba da sanarwar cewa daga yanzu za a rika amfani da takardun kudin Najeriya a hada-hadar kasuwanci a kasar. Matakin da ya yi wa ’yan kasuwar Najeriya dadi matuka. Abu na farko dai shi ne wannan matakin zai rage ko ya kankare tsadar musayar kudaden kasashen waje da Najeriya ke […]

Mahukunta a kasar Birtaniya sun ba da sanarwar cewa daga yanzu za a rika amfani da takardun kudin Najeriya a hada-hadar kasuwanci a kasar. Matakin da ya yi wa ’yan kasuwar Najeriya dadi matuka.
Abu na farko dai shi ne wannan matakin zai rage ko ya kankare tsadar musayar kudaden kasashen waje da Najeriya ke fuskanta, musamman Fam din Ingila da Dalar Amurka. Wadannan kudaden na kasashen biyu sun yi wa kudin Najeriya fintikau a kasashen duniya musamman a kasuwannin kasashen waje.
Tuni dai masana harkar tattalin arziki suka fara sharhi A kan wannan ci gaba da Najeriya ta samu, inda wadansu ke ganin cewa wannan mataki zai taimaka wa Najeriya ta fuskoki da dama, sannan zai kara tagomashi ga kudin Najeriya kuma ya samar da bunkasar tattalin arziki musamman a wannan lokaci da darajar Naira ta fado kasa ainun.