Za a fara bikin kalankuwar ’yan fim a Kano

MOPPAN za ta fara tallafa wa kananan jaruman Kannywood ta hanyar ba su horo.

Za a fara bikin kalankuwar ’yan fim a Kano

Sakataren Kungiyar MOPPAN, Darakta Kamal S. Alkali

Kungiyar Masu Shirya Fina-finan Hausa (MOPPAN) reshen Jihar Kano ta shirya domin gudanar da bikin kalankuwar ’yan fim a bana.

MOPPAN ta ce a bana za ta fara ba wa kananan jaruman Masana’antar Kannywood ta hanyar ba su horo a ciki da wajen Najeriya baya ga shirya bikin kalankuwa.

Sakataren kungiyar, Darakta Kamal S. Alkali ne ya bayyana hakan, inda ya ce, “Kungiyar MOPPAN, reshen Jihar Kano za ta tallafa wa kananan forodusoshi da jarumai a cikin wannan shekara.

“Akwai kuma tsarin bayar da horo da da tura ’yan Kannywood zuwa kasashen waje da kuma shirya taron kalankuwa wato festival.”

Wannan sanarwar ta dadada wa masu bibiyan masana’antar, kamar Darakta Hassan Giggs, inda ya ce, “Wannan tsari ne mai kyau. Allah Ya dafa.”

Shi ma forodusa Abdul Amart cewa ya yi cikin barkwanci, “Ina za mu zo mu karba?”

Ba wannan ba ne na farko

Sai dai ba wannan ba ne na farko da ake maganar tallafa wa kananan jaruman da forodusoshi a masana’antar.
Ko a shekara biyu baya ‘yan fim sun ziyarci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, inda aka ce za a ba da tallafi, wanda daga baya aka koma nuna wa juna yatsa.

‘Yaudara ce kawai, ba za su iya ba’

Wani jarumi kuma forodusa a Kannywood din da Aminiya ta zanta da shi kan lamarin, ya ce yaudara ce da karya suke yi, amma ba za su iya ba.

A cewarsa, “Ba karamin kudi za a kashe ba a irin wannan lamari, kuma babu kudin a kasa.

“Sannan ko an samu kudin, karshe za a koma ne ana son kai wajen zabar wadanda za su ci moriyar lamarin.”

Shi ma forodusa Alhaji Sheshe cewa ya yi cikin Ingilishi ‘lol, interested.” Wanda ke nuna akwai magana.