Za a fara biyan kudin kallon talabijin a Ghana

Daga watan gobe na Agustan bana, mutanen kasar Ghana za su fara biyan kudin kallon talabijin da suka mallaka a gidajensu kamar yadda ake yi a wasu kasashen duniya. Tsarin na gwamnatin Ghana ya nuna cewa mai akwatin talabijin daya a gidansa zai rika biyan Dala tara (kimanin Naira dubu biyu) a duk shekara.Sai kuma […]

Za a fara biyan kudin kallon talabijin a Ghana
Za a fara biyan kudin kallon talabijin a Ghana

Daga watan gobe na Agustan bana, mutanen kasar Ghana za su fara biyan kudin kallon talabijin da suka mallaka a gidajensu kamar yadda ake yi a wasu kasashen duniya.

Tsarin na gwamnatin Ghana ya nuna cewa mai akwatin talabijin daya a gidansa zai rika biyan Dala tara (kimanin Naira dubu biyu) a duk shekara.
Sai kuma duk wanda ke da fiye da talabijin biyu a gidansa, zai rika biyan Naira 3,500 duk shekara.
A shekarar 2010 ne aka bullo da wannan shiri amma aka dakatar saboda matsala wajen karbar kudin daga wurin jama’a.
Gwamnatin Ghana ta ce kashi 72 cikin 100 na kudin kallon talabijin din za a bai wa kafar watsa labarai ta gwamnatin Ghana, a yayin da za a bai wa kafafen watsa labarai masu zaman kansu kashi 15 cikin 100 na kudin da aka tara.
Mutanen kasar Ghana dai sun nuna mamaki game da daukar wannan matakin, inda a cewarsu shirye-shiryen kafafen yada labaran kasar ba sa kayatar da su da har za a ce su rika biyan kudin kallonsu.
Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da kimanin lauyoyi 150 daga dukan jihohin kasar ta Ghana suka fara yajin aiki a shekaranjiya Laraba.
Lauyoyin sun yajin aikin ne domin su matsa lamba wa gwamnati ta kara musu albashi, sannan ta sanya su a cikin tsarin karbar fansho.
Yajin aikin zai kawo tsaiko a kan shari’ar manyan laifuffuka da ake gudanarwa a kasar.
kasar Ghana na fama da matsalolin tabarbarewar tattalin arziki, lamarin da ya sa take daukar matakan tsuke bakin-aljihu.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos