Za a fara daukar sabbin ‘yan N-Power —Minista

Gwamnatin Tarayya ta sanar da lokacin daukar sabbin matasa a shirin aikin N-Power yayin da wa’adin matasa 5000 da ke amfana da shirin a yanzu ke dab da cika. Ministar Ayyukan Agaji da Jinkai, Sadiya Umar Faruk ta ce, “Za a fara dibar sabbin ‘yan N-Power daga ranar 26 ga watan Yulin 2020, amma za […]

Za a fara daukar sabbin ‘yan N-Power —Minista

Ministar Jinkai da Agajin Gaggawa, Hajiya Sadiya Umar Faruk

Gwamnatin Tarayya ta sanar da lokacin daukar sabbin matasa a shirin aikin N-Power yayin da wa’adin matasa 5000 da ke amfana da shirin a yanzu ke dab da cika.

Ministar Ayyukan Agaji da Jinkai, Sadiya Umar Faruk ta ce, “Za a fara dibar sabbin ‘yan N-Power daga ranar 26 ga watan Yulin 2020, amma za a bude dauka ta intanet daga karfe 12 na daren 26 ga watan Yuni”.

Sanarwar da tafita ta ce rukunin farko na matasa da ke cikin shirin a yanzu za su ajiye aiki a ranar 31 ga watan Yuni, rukuni na biyu kuma a ranar 31 ga watan Yulin 2020.

Matasa 2,000 ne suka shiga rukunin farko na shirin a watan Satumbar 2016, kafin wasu 3,000 su shiga a rukuni na biyu a watan Agustan 2018.

A baya an tsara rukunin farko za su yi watanni 24 ne, amma rukunin ya kwashe watanni 40 a tsarin na N-power.

A kwanakin baya ne wasu da suka amfana da shirin suka yi ta korafin rashin samun albashinsu na tsawon watanni uku.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara