Za a fara gasar kwallon cin kofin Bishop Mike Okonkwo a Legas
kungiyoyin kwallon kafa 48 daga ihar Legas da Ogun da kuma Oyo za su fafata a gasar da cocin Trem ta shirya don cin kofin babban limamin cocin mai suna Bishop Mike Okonkwo a Jihar Legas. Gasar wacce ita ce karo na 13 za a fara a ranar Asabar mai zuwa a filin wasa na […]
kungiyoyin kwallon kafa 48 daga ihar Legas da Ogun da kuma Oyo za su fafata a gasar da cocin Trem ta shirya don cin kofin babban limamin cocin mai suna Bishop Mike Okonkwo a Jihar Legas.
Gasar wacce ita ce karo na 13 za a fara a ranar Asabar mai zuwa a filin wasa na kasa da kasa da ke jihar Legas.
Dukkanin wasannin ban da wasan karshe za a gudanar da su ne a filin wasa na kasa da kasa da ke jihar Legas.
Shi kuwa wasan karshe na fainal za a yi shi ne a ranar 29 ga watan Agustan shekarar 2015 a kwalejin kimiyya ta Yaba da ke jihar.
Sai dai rahotannin da Aminiya ta tattaro sun nuna cewa kungiyoyi 11 daga cikin kungoyoyin da za su fafata a gasar suna da alaka da coci-coci kamar cocin Redeemed Ebangelical Misssion da cocin Redeemed Christian Church Of God da kuma cocin Aglican.
Amma sauran kungogyin kwallon kafar na kungiyoyin ne masu zaman kansu har ma wasu daga cikinsu suna da alaka da kungiyoyin kwallon kafa na kasashen wajen.
Shugaban kwamitin tsare-tsare na gasar, Malachy Ndubuzor ya ce ’yan wasa dubu daya da 36 ne za su nuna bajintar su a gasar.
Ya bayyana cewa za a bayar da sabon kofi wanda kamfanin Fumman ya bayar a madadin bukin ranar haihuwar bishop Mike Okonkwo a watan Satumba.