Za a fara ladabtar da duk malamin addinin da ya ‘kirkiro sabon abu’ a Oyo

Majalisar Al’ummar Musulmi a Jihar Oyo ta kafa kwamitin ladabtar da dukkan malamin da aka samu da laifin shigo da sabon abun da ya saba da koyarwar addinin Musulunci a Jihar. Babban Limamin Ibadan kuma Shugaban Kungiyar Limamai da Malamai reshen Jihar ta Oyo, Sheikh Abdulganiyu Abubakar Agbotomokekere, ne zai jagoranci kwamitin ladabtarwar a matsayin […]

Za a fara ladabtar da duk malamin addinin da ya ‘kirkiro sabon abu’ a Oyo

Majalisar Al’ummar Musulmi a Jihar Oyo ta kafa kwamitin ladabtar da dukkan malamin da aka samu da laifin shigo da sabon abun da ya saba da koyarwar addinin Musulunci a Jihar.

Babban Limamin Ibadan kuma Shugaban Kungiyar Limamai da Malamai reshen Jihar ta Oyo, Sheikh Abdulganiyu Abubakar Agbotomokekere, ne zai jagoranci kwamitin ladabtarwar a matsayin Shugaba.

Daukar wannan mataki da al’ummar Musulmin suka yi, ya biyo bayan kama korarren Na’ibin babban Masallacin kauyen Awotan ne da mutane biyu da jami’an tsaro suka zarge su da kashe wani mutumi da suka daddatsa sassan jikinsa domin yin tsafi.

Da yake yi wa ‘yan jarida bayani a wajen wani taro a ranar Asabar, Shugaban Majalisar Al’ummar Musulmin Jihar, Alhaji Ishaq Kunle Sani, ya ce majalisar za ta ci gaba da bibiyar al’amarin wannan korarren Na’ibi har zuwa lokacin da za a yanke masa hukunci.

Ya ce kwamitin ladabtarwar zai yi aikin binciken kwakwaf ga dukkan limamai da malaman da aka zarge su da aikata laifin shigo da sabon abun da ya sabawa koyarwar Musulunci.

Kunle Sani ya yi kira ga Musulmai da ke zaune a unguwanni daban-daban da su dauki matakin kai karar dukkan limami ko malamin da suke zarginsa da aikata miyagun ayyuka ga jami’an tsaro.

“Kada ku dauki doka a hannunku. Idan kun ga wani daga cikinsu yana almubazzaranci da kudi ku sanar da jami’an tsaro. A nan gaba dukkan wanda za a nada domin jagorantar al’ummar Musulmi ya zama wajibi mu yi kyakkyawan binciken kan tarihinsa,” in ji shi.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan