Za a fara rigakafin kenda a jihohi 19
Gwamnatin Tarayya za ta fara zagon farko na rigakafin cutar kenda na bana da Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma jihohi 19 da ke yankin arewacin kasar nan a karshen watan gobe. A lokacin shirin za a yi wa yara ’yan kasa da shekara biyar allurar rigakafin daga ranakun 21 zuwa 25 ga watan Nuwambar […]
Gwamnatin Tarayya za ta fara zagon farko na rigakafin cutar kenda na bana da Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma jihohi 19 da ke yankin arewacin kasar nan a karshen watan gobe.
A lokacin shirin za a yi wa yara ’yan kasa da shekara biyar allurar rigakafin daga ranakun 21 zuwa 25 ga watan Nuwambar bana. Har ila yau, za a gudanar da zango na biyu a jihohi 17 da ke yankin kudancin kasar nan daga ranakun 28 ga watan Janairu zuwa 1 ga watan Fabrairun badi.
Har ila yau, an hasashen shirin zai lashe kusan naira biliyan 10. Inda ake fatan yara kimanin miliyan 40 ne za su karbi rigakafin, a burin da ake da shi na kawar da cutar nan da shekarar 2020 wato kimanin nan da shekaru biyar masu zuwa, kamar yadda Daraktan Gudanarwa na Hukumar Lafiya a Matakin Farko Dokta Ado Muhammad ya bayyana lokacin ganawa da ’yan jarida a Abuja, ranar Litinin.
Kamar yadda Dokta Adamu Nuhu wanda ya wakilci daraktan ya bayyana, wannan shirin zai kara bai wa yaran da ba su samu allurar rigakafin ba damar yin hakan a wannan lokaci. Har ila yau, ya ce “rigakafin yana da matukar muhimmanci bisa la’akari da yadda cutar Bakon Dauro take haifar da makanta da kuma kasance cewa cikin sahun cututtuka biyar masu saurin halaka yara.”
A bana akwai akalla yara 7,538 wadanda suka harbu da kwayar cutar a fadin kasar nan. Kodayake, sabanin yadda aka saba gani a lokacin rigakafin cutar Shan-inna, inda ma’aikatan lafiya suke zuwa gida-gida don bai wa yara rigakafin. A wannan karon za a bude cibiyoyin wucin gadi da na dindindin guda 52, 323 wadanda za su kasance kusa da al’umma. “Makarantu da masallatai da majami’u da sauransu suna cikin wuraren da za a bude irin wadannan cibiyoyi,” inji shi.