Za a fara wasan kwallon gora a Jigawa

Shirye shirye sun yi&nbsp nisa wajen fara gasar kwallon gora (Hockey) na Mai Martaba Sarkin Dutse a filin kwallon hoki na Mai Martaba Sarkin Dutse da ake shirin yin arangama a watan gobe. Kyaftin Adoke ne ya fadi haka a lokacin da ya kai wa Gwamna Badaru Abubakar ziyarar ban girma bayan ya duba yanayin […]

Za a fara wasan kwallon gora a Jigawa
Za a fara wasan kwallon gora a Jigawa

Shirye shirye sun yi&nbsp nisa wajen fara gasar kwallon gora (Hockey) na Mai Martaba Sarkin Dutse a filin kwallon hoki na Mai Martaba Sarkin Dutse da ake shirin yin arangama a watan gobe.
Kyaftin Adoke ne ya fadi haka a lokacin da ya kai wa Gwamna Badaru Abubakar ziyarar ban girma bayan ya duba yanayin filin wasan na Mai Martaba Sarkin da za a gudanar da wasan a bana
Ya bukaci Gwamna Badaru da ya ba su gudunmawar da ta kamata don a samu nasarar gudanar da wasan cikin nasara.
Ya ce sun zo gidan gwamnatin jihar me domin nuna goyan bayansu ga gwamnati bayan sun yi amfani da damar wajen duba yanayin filin wasan.
Da yake mayar da jawabi Gwamna Badaru ya yi alkawarin ba su duk abin da suke bukata don a samu nasarar gudanar da gasar ta hoki.gwamnatin jihar a shirye take wajen ganin ta taimakawa matasa a harkokin wasanni.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa