Za a fara yakar miyagun ayyuka da fasahar zamani
Mukaddashin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Muhammad Abubakar Adamu ya ce, rundunar za ta maye gurbin amfani da makami ta hanyar yin amfani da fasahar zamani wajen yakar laifuffuka. Shugaban ’yan sandan Najeriyar ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da jami’an rundunar da ’yan jarida a makarantar horar da ’yan […]
Mukaddashin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Muhammad Abubakar Adamu ya ce, rundunar za ta maye gurbin amfani da makami ta hanyar yin amfani da fasahar zamani wajen yakar laifuffuka. Shugaban ’yan sandan Najeriyar ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da jami’an rundunar da ’yan jarida a makarantar horar da ’yan sanda da ke Ikeja, Legas a ziyarar da ya kai jihar ranar Litinin da ta gabata, sakamakon kashe-kashen ba gaira ba dalili da wadansu jami’an rundunar ke yi a jihar.
Ya ce, rundunar za ta bullo da sababbin tsare-tsaren ba da horo na musamman ga jami’an rundunar ta fuskar amfani da makami tare da mu’amala da jama’a, “Ko kadan ba za mu lamunce kashe-kashen ba gaira ba dalili ba daga jami’anmu,” inji shi.
Ya mika ta’aziyya ga iyalan budurwar da wadansu ’yan sanda suka harbe a jihar.
A ranar Asabar da ta gabata ce wadansu ’yan sanda da ke aiki da ofishin rundunar na Tirinity a Apapa suka harbi wani saurayi da budurwarsa lokacin da suke dawowa daga wajen liyafar dare a wani kulob din shakatawa. Majiyar Aminiya ta ce ’yan sandan da ake zargi da kisan sun nemi saurayin mai suna Emmanuel Akomafuwa ya tsaya ne lokacin da yake tukin mota a yankin Olodi Apapa, amma ya ki tsayawa lamarin da ya sanya ’yan sandan da ake zargi suka harbe shi a kai ganin haka sai budurwar tasa Ada Ifeanyi mai shekara 20 ta yi wa ’ya sandan ihu inda suka harbe ta ta mutu nan take, yayin da saurayin mai shekara 32 ya jikkata ake kokarin ceto rayuwarsa a asibiti.
A wata sanarwa da Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas DSP Bala Elkana ya fitar ya ce rundunar ta kama ’yan sanda 5 da ake zargi da harbin saurayi da budurwar.
Wadanda aka kama sun hada da Sufeta Adamu Usman da Saje Adeyeye Adeoye da Saje Kashim Tijjani da Saje Lucky Akigbo da kuma Saje Paul Adeoye yayin da Sufeta Dania Ojo ya gudu ana nemansa.
Ya ce, zuwa yanzu ana ci gaba da bincikar wadanda ake zargin kuma za a ladabtar da su, “Ko a baya ma a Jihar Legas an kori jami’an ’yan sandan hudu daga bakin aikin bayan an same su da laifuffukan da suka hada da amfani da makami ba bisa ka’ida ba inda aka garkame su a gidan yari bayan sun gurfana a kotu, an kuma yi wa ’yan sanda 41 hukunci mai tsauri,” inji shi.
Ya ce, ko kadan rundunar ba za ta lamunci kisan mummuke ko na kan mai uwa da wabi da wadansu bata gari ke yi a cikin jami’an rundunar.