Za a fara yi wa manyan Najeriya rigakafin Coronavirus karo na biyu

Kwamitin ya bayyana ranar Talata a matsayin ranar da fara karbar rigakafin allurar.

Za a fara yi wa manyan Najeriya rigakafin Coronavirus karo na biyu

Kwamitin da Shugaban Kasa ya kafa don yaki da cutar Coronavirus, ya ce za a fara zagaye na biyu na rigakafin cutar a ranar Talata a Abuja.

Hakan na zuwa ne bayan kwamitin wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Boss Mustapha ke jagoranta ya samu amincewar Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC).

  1. ’Yan bindiga sun sace shugaban APC a Neja
  2. Sojoji sun kashe ’yan bindiga 78 a dazukan Zamfara

Mai magana da yawun Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF), Mista Willie Bassey ne ya bayyana hakan a ranar Asabar cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai

“Kwamitim PSC ya karbi alluran rigakafin Moderna sama da miliyan hudu daga Gwamnatin Amurka.

“An shirya fara yin zagayen allurar rigakafin daga ranar Talata, 10 ga Agusta, a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Jabi a Abuja,” in ji sanarwar.

Gwamnatin Amurka ce ta ba da tallafin allurar rigakafin ga Najeriya kuma an kawo su ta hanyar COVAX a ranar 2 ga Agusta, 2021.

COVAX wani yunkuri ne na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya yi alkawarin samar da alluran rigakafin zuwa kashi 20 ga kasashen duniya.

Tun a watan Mayu Shugaban Amurka, Joe Biden ya yi alkawarin raba alluran rigakafin miliyan 80 ga kasashen duniya don kare marasa galihu, wadda ake sa ran Afirka za ta samu miliyan 25 daga cikin miliyan 80 da za a raba.

Haka kuma, a watan Maris ne Gwamnatin Najeriya ta karbi allurar miliyan hudu na AstraZeneca, wanda aka yi wa mutum 3,938,945 daga cikin jihohi 36 da Birnin Tarayya.

Ana sa ran fara yi wa manyan shugabannin Najeriya rigakafin allurar na Moderna, inda kuma aka hana yi wa ’yan kasa da shekara 18 rigakafin allurar.