Za a fassara huɗubar Arafa cikin harsuna 20 — Saudiyya
Hausa ne kaɗai harshen da ya samu damar shiga jerin harsunan da za a yi fassara da su a duk faɗin Najeriya.
Mahukunta Masallatan Alfarma na Saudiyya, sun bayyana jerin harsuna 20 da za a yi amfani da su wajen fassara huɗubar ranar Arafa ta bana.
Shafin Haramain Sharifain ne ya tabbatar da hakan cikin wani sako da ya wallafa a wannan Juma’ar.
- Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun hutun Babbar Sallah
- Za mu bai wa Ukraine rancen dala biliyan 50 a kadarorin Rasha — G7
Ya bayyana cewa za a fassara huɗubar Arafa ta gobe Asabar da misalin ƙarfe 12:20 na rana agogon Saudiyya.
A cikin jerin harsunan har da Hausa, wanda ya zama guda ɗaya tilo da ya samu shiga jerin harsunan a duk faɗin Najeriya.
A shekarun bayan nan dai an rika fassara huɗubar ranar Arafa cikin harsuna daban-daban, inda kusan shekaru huɗu da suka gabata harshen hausa ya samu shiga.
Ga jerin harsunan da za a yi amfani da su wajen fassarar hudubar ta bana:
1. Ingilishi
2. Faransanci
3. Malay
4. Urdu
5. Persian/ Farsi
6. Cananci
7. Turkish
8. Russian
9. Hausa
10. Bengali
11. Swedish
12. Sfaniyanci
13. Swahili
14. Amharic
15. Italian
16. Portuguese
17. Bosnian
18. Malayalam
19. Filipino
20. Jamusanci
Fiye da musulmi miliyan ɗaya da rabi ne daga sassa daban-daban na duniya suka soma ibadar aikin Hajji yau Juma’a a ƙasa mai tsarki.
Bayanai na nuna yiwuwar musulmin da za su gudanar da wannan ibada daga ciki da wajen saudiya su iya haura miliyan 2, bayan da mahukuntan ƙasar suka sanar da kame fiye da mahajjata dubu 300 da suka shiga don yin ibadar ba bisa ƙa’ida ba.
A gobe Asabar ce ɗimbin musulmin ke shirin hawan Arafa, wato ginshiƙin ibadar ta aikin Hajji.
Sai dai a wannan karon Hajjin na zuwa a wani yanayi da duniyar musulunci ke kokawa da halin da Falasɗinawa ke ciki sakamakon kisan ƙare dangin da suke fuskanta daga Isra’ila a Gaza da zuwa yanzu ya kai ga kisan musulmin dubu 38.