Za a gina cibiyar dashen hanta a Kano, wadda babu irinta a Afirka ta Yamma

Za a gina cibiyar dashen hanta wadda babu irinta a fadin Afrika ta Yamma a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ke Jihar Kano.

Za a gina cibiyar dashen hanta a Kano, wadda babu irinta a Afirka ta Yamma

Asibitin Malam Aminu Kano

Za a gina cibiyar dashen hanta wadda babu irinta a fadin Afrika ta Yamma a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ke Jihar Kano.

Shugaban kamfanin Iyaka Rabi’u & Sons, Rabi’u Iaiyaka Rabi’u ya bayyana cewa baya ga aikin koda, cibiyar za ta kuma rika kula da masu cututtukan da suka danganci cikin dan Adam.

Ya sanar Da haka a jawabinsa ga babban taron masana kimiyyar lafiyar ciki da hanta (SOGHIN) da aka gudanar a Kano ranar Alhamis.

Ya ce za a gina cibiyar ce da hadin gwiwar gwamnati da attajiran jihar, kuma ana sa ran za ta yi zarra wajen biyan bukata ba a Kano kadai ba, har a fadin Najeriya.

“Mun jima muna tattaunawa da shugabannin Asibitin Koyarwa na Aminu Kano na da da na yanzu kan wannan batu.

“Saboda Ni da kaina zan jawo ’yan uwa da abokan arziki da sauran masu kishi wajen gina Cibiyar Dashen Hanta ta Kasa a Kano

“Zan kuma jawo dan uwansa kuma Shugaban Rukunin Kamfanonin BUA, Abdussamad Isyaka Rabi’u ya taimaka sosai da kudade wajen aiwatar da wannan aikin.

“Ina fata nan gaba Kano za ta yi zarra ba wai a fannin dashen koda ba kawai, har sada sauran cututtukan ciki a yankin Arewa maso Yamma da ma Najeriya baki daya.

“Wadannan su ne irin abubuwan da ya kamata mu yi wa al’umma domin cika burukan likitocinmu,” inji shi.

Tun da farko shugaban kungiyar SOGHIN ta Kasa, Jessy Abiodun Otegbayo, ya ce kashi 40 cikin 100 na masu zuwa ganin likita a fadin duniya, ciwon ciki da dangoginsa ke damun su.

Da yake masa jawabi, Shugaban Asibitin Koyarwa na Aminu Kano,  Farfesa Abdulrahman Abba Sheshe, ya ce asibitin ya gudanar da dashen koda cikin nasara 100 bisa 100.