Za a gina tashoshin lantarki mai amfani da hasken rana a Arewa

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu ya ce, Gwamnatin Tarayya za ta gina babbar tashar wutar lantarki mai amfani da hasken rana a kowace jiha da ke Arewacin Nijeriya. A halin yanzu saura goma babban layin wutar lantarkin Nijeriya yake ɗaukewa a a cikin wata 10 na wannan ta 2024. Adelabu ya ce, gwamnatin ta fara […]

Za a gina tashoshin lantarki mai amfani da hasken rana a Arewa

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu ya ce, Gwamnatin Tarayya za ta gina babbar tashar wutar lantarki mai amfani da hasken rana a kowace jiha da ke Arewacin Nijeriya.

A halin yanzu saura goma babban layin wutar lantarkin Nijeriya yake ɗaukewa a a cikin wata 10 na wannan ta 2024.

Adelabu ya ce, gwamnatin ta fara tattaunawa da ’yan kwangila kan yiwuwar samar da megawat 100 na wuta a duk jihar da ke yankin, duba da albarkar hasken rana da Allah Ya hore musu.

Ministan ya ce, za a gina tashoshin ne da nufin tabbatar da samuwar tsayayyiya kuma wadatacciyar wutar lantarki a faɗin yankin Arewa.

Ya bayyana haka ne bayan wata ganawa da Shugaba Bola Tinubu ya yi da shi da shugabannin tsaro kan lalacewar wutar yankin na kimanin kwana 10.

Ministan ya ce, Tinubu ya umarci Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa da Mashawarcinsa Kan Tsaro su bayar da duk tsaron da ya kamata domin gyara wutar Arewar.

An shafe sama da mako guda cikin duhu a Arewa, sakamakon lalacewar babban layin lantarkin da ke kawo wuta yankin, wanda ya taso daga Shiroro zuwa Kaduna.

Kamfanin Wutar Lantarki na Ƙasa (TCN) ya sanar cewa, ’yan ta’adda ne suka lalata layin wutar, kuma zuwa wurin na da matuƙar haɗari, amma suna aiki da hukumomin tsaro domin bayar da kariya ga ma’aikata domin gyara wutar.

Adelabu ya ƙara da cewa, Majalisar Zartarwa ta Ƙasa ta amince a sabunta tare da ƙara ƙarfin layin wutar na Shiroro zuwa Kaduna, wanda shi ne mafi daɗewa a Nijeriya kuma shi ne tushe wutar Arewa.

Ya ba wa al’ummar yankin haƙuri game da matsalar.

Ya ce, zai tabbatar ba za a caje su kuɗin wutar da ba su sha ba a tsawon lokaci, kuma zai tattauna da Hukumar Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) da kamfanonin rarraba wutar kan game da hakan.

Ya kamata a ayyana dokar ta-ɓaci – ACF

Ƙungiyar Kare Muradun Arewa ta ACF ta buƙaci Shugaba Tinubu ya gaggauta ayyana dokar ta-ɓaci kan yawan ɗauke wuta a yankin, wanda ta bayyana a matsayin barazana ga tsaron ƙasar.

Ƙungiyar ACF ta kuma caccaki gwamnatin kan dora laifin rashin gyara wutar a kan matsalar tsaro.

Sanarwar ta kakakin ƙungiyar, Farfesa Tukur Muhammad-Baba, ta ce, “uzurin cewa akwai rashin tsaro a wajen da wutar ta lalace ba komai ba ne face nuna cewa yankin yana ƙarƙashin ’yan ta’adda.’’

Ya kuma yi zargin ana cutar da Arewa wajen rabon wutar, inda ya ce abin da ake ba wa yankin bai taka kara, ya karya ba.

“Abin mamaki shi ne, daga Arewa ake samar da ƙarfin wuta mai yawan gaske, amma kason da yankin ke samu shi ya fi ƙanƙanta.

Hankali ba zai ɗauka ba a ce Legas kaɗai na da tashoshin lantarki takwas, amma ɗaukacin yankin Arewa, wanda ya fi rabin Nijeriya, yake da guda uku kacal.

Don haka ƙungiyar ta buƙaci a sake duba tsarin rabon wutar ƙasar domin ba zai yiwu kura da shan bugu, gardi da amshe kuɗi ba.