Za a gina titin jirgin kasa mai nisan kilomita 38 a Ibadan

Gwamnatin Jihar Oyo ta kulla yarjejeniya da wani kamfanin kasar China (CCECC), da zai yi aikin shimfida layin dogo mai nisan kilomita 38 a cikin birnin Ibadan. Kwamishinan ayyuka da sufuri na Jihar Oyo, Mista Wasiu Dauda ne ya sanya hannu a madadin gwamnati a yayin da Mista Jack Lyao ya sanya hannu a madadin […]

Za a gina titin jirgin kasa mai nisan kilomita 38 a Ibadan

Gwamnatin Jihar Oyo ta kulla yarjejeniya da wani kamfanin kasar China (CCECC), da zai yi aikin shimfida layin dogo mai nisan kilomita 38 a cikin birnin Ibadan. Kwamishinan ayyuka da sufuri na Jihar Oyo, Mista Wasiu Dauda ne ya sanya hannu a madadin gwamnati a yayin da Mista Jack Lyao ya sanya hannu a madadin kamfaninsa.

Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo, wanda aka sanya hannu a kan yarjejeniyar a kan idanunsa ya ce, wannan aiki na layin jirgin kasa mai gajeren zango zai rage cunkoson abubuwan hawa kwarai a birnin na Ibadan kuma zai taimaka wajen bunkasar harkokin kasuwanci da sufuri da tattalin arzikin jihar.

Gwamnan ya nemi jama’a, musamman wadanda aikin shimfida layin dogon zai ratsa ta cikin unguwanni da gidajensu da su tabbatar da hadin kai da goyon baya a lokacin da aka fara aikin. Ya ce wannan aiki ne da zai taimaka wa mazauna Ibadan da Jihar Oyo baki daya.

Shi kuwa Kwamishinan ayyuka da sufuri Mista Wasiu Dauda, cewa ya yi kamfanin na kasar China mai suna CCGCC shi ne zai nemo kashi 85 na yawan kudin da za a kashe a kan wannan aiki, a yayin da gwamnatin jihar za ta samar da kashi 15 a matsayin gudunmawarta.

Kwamishinan ya yi fatan ganin cewa a cikin watanni 4, kamfanin ya samu bashin kudin da yake bukata wajen gudanar da aikin. Ya ce aikin shimfida layin dogon zai faro ne daga matsayar motoci ta Toll Gate a Ibadan zuwa Unguwar Sanyo da zai wuce zuwa titin kueen Elizabeth da Dandaru a Unguwar Mokola tare da zarcewa zuwa matsayarsa a Ojoo.

“Za a fara gudanar da aikin ne daga ranar da kamfanin ya samu karbar bashin kudin aikin daga bankunan kasuwanci kuma ana kyautata zaton kammala aikin a cikin watanni 12 ne,” inji kwamishinan.

Jagoran tawagar kamfanin na CCGCC Mista Jack Lyao ya bayar da tabbacin ganin sun kammala aikin a cikin watanni 12 da suka yi alkawari.