Za a gina wa ’yan gudun hijirar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sansani a Jihar Gombe

Jihar Gombe ta yi alkawarin samar da sansani na wucin gadi ga ’yan gudun hijirar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ’yan asalin Najeriya da suke gudun hijira a Jamhuriyar Kamaru a karamar Hukumar Funakaye da ke jihar.Babban Sakataren Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe Mista danlami Arabs Rukuje ne ya bayyana haka a lokacin da […]

Za a gina wa ’yan gudun hijirar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sansani a Jihar Gombe
Za a gina wa ’yan gudun hijirar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sansani a Jihar Gombe

Jihar Gombe ta yi alkawarin samar da sansani na wucin gadi ga ’yan gudun hijirar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ’yan asalin Najeriya da suke gudun hijira a Jamhuriyar Kamaru a karamar Hukumar Funakaye da ke jihar.
Babban Sakataren Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe Mista danlami Arabs Rukuje ne ya bayyana haka a lokacin da yake kaddamar da raba kayayyakin tallafi ga wadanda bala’in iska ya shafa a kananan hukumomin jihar hudu.
Mista danlami Rukuje, yace akwai kimanin ’yan gudun hijira ’yan Najeriya kimanin 601 da yanzu haka suke gudun hijira a Jamhuriyyar Kamaru da ake son a dawo da su Najeriya kafin a maida kowannensu jiharsa .
A cewarsa a ranar g17 ga Afrilun bana ne aka samu bala’in iska da ta fada wa kananan hukumomin Akko da billiri da Kaltungo da kuma Gombe, inda ya shafi mutum 2,261a kananan hukumomin hudu, kuma kowannensu za a ba shi kwanon rufi bandir biyu da buhun siminti biyu don saukake masa wahala wanda a cewarsa ba an biya su diyya ba ne.
Mista Rukuje, ya kara da cewar kafin wadannan a cikin wata biyu da suka gabata hukumar ta ba da tallafi ga mutane kimanin 1,800 da bala’i ya shafa a fadin jihar.
Daga nan sai ya kirayi shugabanin kananan hukumomin jihar da su rika ba da irin tasu gudunmawar ga wadanda bala’i ya shafa don saukaka musu daidai gwargwado.
Ya ce duk wanda bala’i ya shafa kuma ba ya da wanda zai taimaka masa su a hukumance suna iya kama wa mutum gidan haya na wata uku zuwa shida kafin ya samu yadda zai yi.
Kimanin Naira miliyan 44 ne gwamnatin jihar ta kashe wajen sayo kayayyakin agajin da aka raba wa wadanda bala’in iskar ta shafa a jihar.