Za a gudanar da gasar karatun Alkur’ani na kasa a Jihar Edo

Hukumar kula da Sashin Musabakah ta karatun Alkur’ani a Jihar Edo ta bayyana cewa ta kamamla shirye-shiryen shiga gasar karatun Alkur’ani na kasa, wanda ake sa ran yi a shekara ta 2015 a garin Auchi Jihar Edo. Hukumar musabakar ta ce tuni har ta tantance masu shiga gasar karatun na shekara ta 2015 mai zuwa,inda […]

Za a gudanar da gasar karatun Alkur’ani na kasa a Jihar Edo
Za a gudanar da gasar karatun Alkur’ani na kasa a Jihar Edo

Hukumar kula da Sashin Musabakah ta karatun Alkur’ani a Jihar Edo ta bayyana cewa ta kamamla shirye-shiryen shiga gasar karatun Alkur’ani na kasa, wanda ake sa ran yi a shekara ta 2015 a garin Auchi Jihar Edo.

Hukumar musabakar ta ce tuni har ta tantance masu shiga gasar karatun na shekara ta 2015 mai zuwa,inda ta zakulo mutum 12, wadanda shida daga cikinsu mata ne, sauran shidan kuma maza ne, wadanda a gasar karatun na jihar suka samu nasarar hayewa, don haka sun samu kyaututtuka da dama da suka hada da kudi, tare da tukunyar irkin zaman ta ‘ gas cooker’ da talabijin na bango (plasma T.b) da fanka wanda ake kira (Industrial Standin Fans).
Musabakar, wadda Mai martaba Alhaji H.A Momoh Otaru na Auchi ya kaddamar, Alkalai shida ne suka saurari masu karatun musabakar, kuma Babban alkalin shi ne, Sadik Assadik daga zamfara; kuma an yi wannan musabakar ne akan izu biyu da izu 10 da izu 20 da 40 har zuwa izu 60, da kuma izu 60 tare da tafsiri.
Otaru na Auchi ya ce wannan musabakar da aka yi ta nuna matsayin sanin addini, inda ya ce wannan zai kawo zaman lafiya a cikin rayuwar mutane, sannan kuma ya ce wannan kira ne zuwa ga fadin Allah Madaukakin sarki. Sannan a cewarsa, wannan abin farin ciki ne ga daukacin al’ummar Jihar Edo tun da sun kaddamar da musabakah ta kasa a karo na biyu cikin shekaru shida kacal. Daga nan kuma sai ya yi kira ga iyaye da su kara wa ‘ya’yansu kwarin gwiwa wajen masabakah.
Shi kuwa kwamishinan albarkatun gona na jihar , Honarabul Abdulrauf ya yi jawabi a taron a madadin Gwamnan jihar ,inda ya ce:’ “Lallai babu shakka sanin addini da matsayinsa zai kara zaman lafiya ta hanyar da gwamnati za ta taimaka wa addinan.
Shi ma Shugaban taron Barrista Hassan Kadiri, wanda Yarima Daz Momoh ya yi magana a madadinsa, inda ya yi alkawarin baiwa duk wadanda suka yi kokari akan karatun izu 60 na alkura’ni mai girma kyauta mai ban mamaki.
Kwadinatan Musabaka na jihar Edo Sheik Ibrahim Oyarekhua ya roki iyaye da su taimaka wa karatu musabakar dabayar da karfin gwiwa, ta hanyar taimakonsu,sannan ya mikagodiyarsa ga gwamana kan irin taimakon da ya bayar a wannan musabaka da kuma ta kasa wadda za a yi nan gaba, wato daga ranar 7 zuwa 15 ga watan Janairun shekarar 2015 a garin Auchi Jihar Edo.