Za a gudanar da gasar mawakan Musulunci a Kano

Cibiyar Dabo Tb Centre da ke Jihar Kano ta ce ta kammala shirye-shiryenta wajen daukar nauyin wani shirin Rediyo da Talabijin na farko a kasar nan game da gasar rera wakokin Musulunci cikin harshen Hausa.Daraktar Cibiyar Hajiya Fatima Dabo ta bayyana cewa gasar ba wai kawai a tsakanin mawakan Jihar Kano ta tsaya ba, za […]

Za a gudanar da gasar mawakan Musulunci a Kano

????????????????????????????????????

Cibiyar Dabo Tb Centre da ke Jihar Kano ta ce ta kammala shirye-shiryenta wajen daukar nauyin wani shirin Rediyo da Talabijin na farko a kasar nan game da gasar rera wakokin Musulunci cikin harshen Hausa.
Daraktar Cibiyar Hajiya Fatima Dabo ta bayyana cewa gasar ba wai kawai a tsakanin mawakan Jihar Kano ta tsaya ba, za ta hada da dukkan jihohin Arewacin kasar nan 19 ciki har da Abuja.
A cewarta cibiyar ta shirya wannan gasa da nufin tallafa wa matasa wajen dogaro da kai tare da fatan hakan zai samar wa mawakan kasuwa wajen tallata basirarsu a duniya.
Ta kuma ce an zabi harshen Hausa ne saboda yin la’akari da cewa yana daga cikin manyan harsuna a duniya wadanda mafi yawan masu magana da shi suka kasance Musulmi. “Wannan shiri shi ne irinsa na farko cikin harshen Hausa don a magance matsalar da dimbin matasanmu suke fuskanta, inda ake barinsu a baya saboda bambancin harshe da kuma rashin ilimin boko.” Inji ta.
Ta ce za a gudanar da gasar ne a bangarori takwas da suka hada da: Tauhidi da yabon Annabi da fadakarwa da tsoron ranar kiyama da yabon Ahlul baiti da wake a kan da’a da amfanin ilimi da kuma a kan mutanen da suka yi wa Musulunci hidima.
Ta kara da cewa “Don a kara wa masu shiga gasar kaimi an tanadi kyaututtuka da za su zama na shiyya da suka fara daga Naira dubu 500 zuwa Naira miliyan daya. Haka kuma akwai kyaututtuka da za a ci a karshen kammala gasar, inda aka ware Naira miliyan uku ga wanda ya samu nasara da Naira miliyan biyu ga wanda ya zo na biyu, sai kuma Naira miliyan daya ga wanda ya zo na uku.
Ana sa ran fara gasar nan da watan Mayu.