Za a gudanar da zaben kananan hukumomi a Bauchi – Udubo

Wani fitaccen dan siyasa daga yankin karamar Hukumar Gamawa, Honarabul Adamu Dauda Udubo ya shawarci al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu domin Gwamnan jihar Barista Mohammed Abubakar zai gudanar da zaben kananan hukumomi nan ba da dadewa ba, domin lokacin da ya karbi ragamar shugabancin jihar ya samu aljihun gwamnati babu ko sisin kwabo […]

Za a gudanar da zaben kananan hukumomi a Bauchi – Udubo
Za a gudanar da zaben kananan hukumomi a Bauchi – Udubo

Wani fitaccen dan siyasa daga yankin karamar Hukumar Gamawa, Honarabul Adamu Dauda Udubo ya shawarci al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu domin Gwamnan jihar Barista Mohammed Abubakar zai gudanar da zaben kananan hukumomi nan ba da dadewa ba, domin lokacin da ya karbi ragamar shugabancin jihar ya samu aljihun gwamnati babu ko sisin kwabo a ciki.

Don haka ya toshe dukkan hanyoyin da ake wasoso da kudin talakawan Jihar Bauchi. Domin ta haka ne zai samu kudin da zai bayar domin a samu damar shirya zaben kananan hukumomi a jihar.
Udubo ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a ofishinsa da ke Bauchi a ranar Litinin din da ta gabata da safe.
A cewarsa, tun daga shekara ta 2008 da aka gudanar da zaben kananan hukumomi a Bauchi ba a sake yin zaben ba, duk da cewa tsohuwar gwamnatin ta samu makudan kudi daga wajen gwamnatin tarayya.
Barista Abubakar mutum ne da ya san doka, muna ba da tabbaci ga al’umma idan aka ba da dukkan goyon bayan da ya kamata ga wannan gwamnati to tabbas kowa sai ya sha romon mulkin dimokuradiyya a Jihar Bauchi da ma Najeriya baki daya.
Honarabul Udubo yana daya daga cikin na hannun damar Gwamna Abubakar a karamar Hukumar Gamawa. Don haka ya tabbatar da cewa zai ci gaba da zantawa da manema labarai daga lokaci zuwa lokaci, domin bayyana wa al’umma kadan daga cikin manufofin gwamnatin ta APC.
Daga karshe ya bukaci al’umma dasu taimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Bauchi da ‘yan majalisu da addu’oi na musamman domin kowa ya san cewa sun karbi gwamnati ne cikin mawuyacin hali.