Za a gudanar da zaben kananan hukumomin Jihar Neja ranar 7 ga Satumba

Hukumar Zabe ta Jihar Neja za ta gudanar da zaben kananan hukumomin jihar a ranar 7 ga Nuwamba mai zuwa.Hukumar ta bayyana haka ne a wata takarda dauke da sanya hannun kakakinta Muhammad Ali. Zaben zai samar da sababbin shugabanni 25 da kansiloli 274 da za su ja ragamar mulki na shekara uku kuma zai […]

Za a gudanar da zaben kananan hukumomin Jihar Neja ranar 7 ga Satumba
Za a gudanar da zaben kananan hukumomin Jihar Neja ranar 7 ga Satumba

Hukumar Zabe ta Jihar Neja za ta gudanar da zaben kananan hukumomin jihar a ranar 7 ga Nuwamba mai zuwa.
Hukumar ta bayyana haka ne a wata takarda dauke da sanya hannun kakakinta Muhammad Ali. Zaben zai samar da sababbin shugabanni 25 da kansiloli 274 da za su ja ragamar mulki na shekara uku kuma zai kasance karo na farko da gwamnatin APC za ta gudanar.
Sanarwar ta ce tun ranar Lahadin makon jiya aka sanar da jam’iyyun siyasa da ke jihar wannan mataki don ba su damar gudanar da tsare-tsarensu da fara kamfe da gudanar da zaben fidda gwani.
Takardar ta nuna cewa a ranar 18 zuwa 19 ga watan Satumba ne hukumar za ta tantance ’yan takarar da jam’iyyun suka tura mata, sannan a ranar 31 ga watan Oktoba ake sa ran jam’iyyun su samar mata sunayen wakilansu da za su fafata a zaben.
A karshe takardar ta ce za ta gudanar da zaben raba-gardama a duk inda bukatar haka ta taso a ranar 14 ga watan Nuwamba a tsakanin jam’iyyar da ke kan gaba da wadda take biye da ita.
Kakakin Hukumar ya shaida wa wakilinmu cewa a shirye take ta gudanar da zaben da al’ummar jihar za su yi alfahari da shi, inda za ta yi amfani da ma’aikatan wucin-gadin da suka don sauke nauyin da ke kanta.

Gwamnoni ku magance talauci da rashin tsaro —Sarkin Musulmi 

Amarya ta yanke maƙogwaron ango a Kano

NAJERIYA A YAU: Masu nau’in jinin AS sun fi masu AA lafiya — Masana

ADC za ta ƙalubalanci hukuncin soke mata rajista