Za a gurfanar da mawaki 442 a gaban kotun Nijar
Ana zargin mawakan ne da mallakar takardun kasar na bogi
Hukumomin jamhuriyar Nijar na shirye-shiryen gurfanar da Mubarak Abdulkarim, wanda aka fi sani da Mista 442 da abokin harkarsa mai suna Mista Ola a gaban kuliya.
Za a gurfanar da mawakan ne bisa zargin mallakar takardun haihuwa na Nijar na bogi.
Alhaji Yusuf Mamman shugaban hukumar gidajen Rediyo da Talbijin na Amfani ne ya tabbatar wa Aminiya hakan a hirar da ta yi da shi a safiyar Talata.
- Lauyoyin Kano sun maka Ado Gwanja da Safara’u a kotu kan lalata tarbiyya
- NAJERIYA A YAU: Kudurin dokar hukunta ’yam madigo da luwadi a kasar Nijar
Alhaji Yusuf ya ce hakika mutanen biyu na tsare tun lokacin da suka shiga hannun jami’an tsaro kimanin makonni biyu da su ka gabata, a inda ake gudanar da binciken kwakwaf a kan su.
Mawakan sun shiga hannu ne a bisa zargin su da mallakar takardun jabu na haihuwar dga Maradi, da kuma kokarin mallakar fasfon kasar domin tafiye-tafiye.
Ya kuma ce, Mawakan sun yi bayyana cewa, wani ne ya yi musu hanyar takardun, da kuma alkawarin samar musu fasfon, jami’an na ci gaba da gudanar da binciken don gano sauran wadanda aka hada bakin da su.
Sun ce da zarar an kamala binciken za a mika su gaban kuliya.
Mallakar takardun dan kasa na bogi a jamhuriyar Nijar babban laifi ne da kan sa kotu ta yi hunkiuci mai tsanani, a cewar wani dan Kasar.