Za a gurfanar da Mendy saboda karensa ya ciji matashi da karnuka biyu

A shekarar 2019 ce Mendy mai shekara 31 ya koma Real Madrid daga ƙungiyar Lyon ta Faransa.

Za a gurfanar da Mendy saboda karensa ya ciji matashi da karnuka biyu

Rahotanni sun bayyana cewa nan gaba kaɗan za a gurfanar da ɗan wasan baya na Real Madrid, Ferland Mendy, a kotu yayin da ake zargin ɗaya daga cikin karnukansa ya kai wa wani matashi da wasu karnuka biyu hari a wajen gidansa da ke Madrid.

Kafofin yaɗa labarai na Spain sun ruwaito masu shigar da ƙara suna neman a yanke masa hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari bisa zargin haddasa rauni kan abin da suka kira sakaci, sannan kuma suna neman a ci tararsa.

Sai dai ofishin mai gabatar da ƙara na gwamnati ya nemi kotu ta ci tararsa kaɗai kan abin da ta bayyana a matsayin ƙaramin laifi.

Bayanai sun ce lamarin ya faru ne a watan Janairun 2023, lokacin da karnuka huɗu mallakin Mendy suka tsere daga gidansa da ke unguwar Alcobendas a birnin Madrid bayan an bar ƙofar gidan a buɗe yayin da wata mota ke shiga.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa, ɗaya daga cikin karnukan ya ciji karen wata mata, wanda daga baya dole aka kashe shi saboda tsananin raunukan da ya samu.

Haka kuma, karen ya ciji wani matashi mai shekara 17 wanda ya yi ƙoƙarin raba rigimar karnukan, sannan kuma ya ciji karen wani ɗan uwansa da yake fita yawo da shi.

A shekarar 2019 ce Mendy mai shekara 31 ya koma Real Madrid daga ƙungiyar Lyon ta Faransa, amma ya sha fama da raunuka da suke daƙile haskensa a wasanni.