Za a gurfanar da mutum biyu don shan taba a jirgin sama
Lamarin ya faru ne a cikin jirgin kamfanin jirgin sama na Air Peace daga Afirka ta Kudu zuwa Legas, lamarin da rahotanni suka ce ya kunna ƙararrawar gaggawa ta gano hayaƙi a cikin jirgin, kuma ya janyo firgici a tsakanin fasinjoji.
Rundunar ’Yan sandan Filin Jirgin Sama na jihar Legas ta bayyana cewa za ta gurfanar da wasu fasinjoji biyu da ake zargi da shan taba sigari da kuma nuna halin rashin tarbiyya.
Lamarin ya faru ne a cikin jirgin kamfanin jirgin sama na Air Peace daga Afirka ta Kudu zuwa Legas, lamarin da rahotanni suka ce ya kunna ƙararrawar gaggawa ta gano hayaƙi a cikin jirgin, kuma ya janyo firgici a tsakanin fasinjoji.
- Mutum 4 sun maƙale, an ceto 3 bayan gini ya rufta a Kano
- Amarya ta rasu yayin da sojoji ke artabu da Boko Haram a Borno
Rundunar ta bayyana hakan ne, a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar (PPRO), ASP Mohammed Adeola ya sanya wa hannu a ranar Juma’a, inda aka gano sunayen waɗanda ake zargin kamar haka: Enaruna Prince Aghama, mai shekara 51 da Tony Ajayi mai shekara 43.
Bisa ga bayanin sanarwar, jami’an tsaron fannin sufurin jiragen sama ne suka mika wadanda ake zargin ga Sashen ’Yan sandan Filin Jirgin Sama bayan jirgin ya sauka a Filin Jirgin Sama na ƙasa da ƙasa na Murtala Muhammed da ke Ikeja, domin gudanar da bincike na gaba.
’Yan sandan sun bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:44 na yammacin ranar Alhamis yayin da jirgin ke kan hanyarsa ta zuwa Legas.
Sanarwar ta ce: “Binciken farko ya bayyana cewa da misalin ƙarfe 7:44 na yamma a ranar 9 ga watan Yuli, 2026, sa’ilin da suke cikin jirgin kamfanin Air Peace daga Afirka ta Kudu zuwa Legas, waɗanda ake zargin sun kunna tare da shan taba sigari a cikin jirgin, matakin da ya kunna na’urar gano hayaƙi da ƙararrawar gaggawa ta jirgin, wanda hakan ya janyo firgici da fargaba a tsakanin fasinjoji da ma’aikatan jirgin.”
Rundunar ta ƙara da cewa binciken ya kuma nuna cewa waɗanda ake zargin suna ɗauke da abin sha mai sa guba (giya), kuma sun ƙi ba da haɗin kai lokacin da ma’aikatan jirgin suka yi ƙoƙarin tabbatar da matakan tsaro.
Sanarwar ta bayyana cewa mutanen biyu “sun ƙi ba da haɗin kai kuma sun nuna halin cacar baki da masifa lokacin da ma’aikatan jirgin suka yi ƙoƙarin kwantar da tarzoma tare da zartar da dokokin tsaro da aka kafa, wanda hakan ya ƙara kawo cikas ga tafiyar jirgin cikin tsari.”
Yayin da take tsokaci kan lamarin, Kwamishinan ‘Yan sanda ta Rundunar Filin Jirgin Sama, CP Ogunbode Olufunke ta bayyana irin halin da ake zargin mutanen da shi a matsayin abin da ba za a amince da shi ba.
Ta ce, “Duk wani aiki da zai iya gurgunta tsaron sufurin jiragen sama ko kuma kawo cikas ga tsarin aikin jirgin sama abu ne da ba za a amince da shi ba.”
