Za a gurfanar da Nuhu Ribadu a gaban Majalisa

Majalisa za ta gayyaci mashawarcin shugaban kasa kan al’amuran tsaro Malam Nuhu Ribadu, saboda lalacewar jiragen Fadar Shugaban Kasa. Shugaban kwamitin lura da jiragen fadar shugaban a Majalisar, Satomi Ahmed,  ne ya sanar da hakan. Alhakin kula da jirgin shugaban kasa da mataimakinsa dai ya rataya ne a wuyan mai bai wa shugaban kasa shawara […]

Za a gurfanar da Nuhu Ribadu a gaban Majalisa

Nuhu Ribadu

Majalisa za ta gayyaci mashawarcin shugaban kasa kan al’amuran tsaro Malam Nuhu Ribadu, saboda lalacewar jiragen Fadar Shugaban Kasa.

Shugaban kwamitin lura da jiragen fadar shugaban a Majalisar, Satomi Ahmed,  ne ya sanar da hakan.

Alhakin kula da jirgin shugaban kasa da mataimakinsa dai ya rataya ne a wuyan mai bai wa shugaban kasa shawara kan al’amuran tsaro.

Honabul Satomi Ahmed ya ce a kwai kasafin na musamman domin kula da jiragen fadar shugaban kasa.

Ya ce wadannan makudan kudade suna karkashin ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ne.

Ya kara da cewa akwai kaso mai tsoka na shekara-shekara daga Majalisar don kula da jiragen.

Satomi ya bayyana damuwarsa, da cewa abin kunya ne halin da jiragen shugaban kasar ke ciki.

Ya ba da misali da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, ciki har da yadda mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya shiga matsala sanadiyyar lalacewar jirgin, wanda dole sai dai ya yi amfani da jirgin haya domim tafiye-tafiye da suka shafi aikinsa.

Satomi ya ce ya kamata ace Najeriya na iya  kula da jiragenta, musamman idan aka yi la’akari da nasarorin da ta samu a baya kamar iya samar da kamfanin Nigeria Airways.