Za a gurfanar da wani hatsabibin bunsuru a gaban kotu

Hukumar Hisba reshen karamar Hukumar Dala a Jihar Kano za ta gurfanar da wani bunsuru da ubangidansa a gaban kotu bisa zargin bunsurun da yi wa mutane fitsari da kashi a kansu a daidai lokacin da suke barci.Mazauna yankin Gwammaja, Layin Kankare a karamar hukumar  ne suka kai korafi gaban Hukumar Hisbar inda suka ce […]

Za a gurfanar da wani hatsabibin bunsuru a gaban kotu
Za a gurfanar da wani hatsabibin bunsuru a gaban kotu

g Hatsabibin bunsurun da za a gurfanar a gaban kotuHukumar Hisba reshen karamar Hukumar Dala a Jihar Kano za ta gurfanar da wani bunsuru da ubangidansa a gaban kotu bisa zargin bunsurun da yi wa mutane fitsari da kashi a kansu a daidai lokacin da suke barci.
Mazauna yankin Gwammaja, Layin Kankare a karamar hukumar  ne suka kai korafi gaban Hukumar Hisbar inda suka ce suna cikin kwanciyar waje saboda yanayin zafin da ake ciki, da zarar karfe 12 :00 na dare ya yi, sai wannan bunsuru ya rika bin kansu yana yi musu kashi da fitsari.
daya daga cikin mutane, Malam Audu Ali ya shaida wa Aminiya cewa bunsurun yana aika-aikarsa ne da zarar ya fuskanci mutanen sun fara nisa a barcinsu. “Da zarar karfe 12:00 ta yi lokacin ya fuskanci kowa daga cikinmu ya yi nisa a barci, sai ya bi kanmu daya bayan daya yana yi mana kashi da fitsari, sai dai in mun tashi da asuba mu yi wanka mu yi Sallah,” inji shi.
Shi kuwa Malam Salisu Muhammad ya ce wani abin al’ajabi da bunsurun shi ne komai yawan jama’ar da ke kwance a wurin to yakan bi kan kowane mutum ya yi masa fitsari da kashi. “Mun dade muna jure bakin cikin da bunsuru ke sanya mu a ciki, kullum muka kwanta sai ya bi kanmu
ya yi mana fitsari da kashi, kuma koda mun kai ashirin a wurin, haka zai bi kanmu daya bayan daya ya yi mana fitsari a kanmu, ina mamakin irin yawan fitsarin da ke jikinsa,” inji shi.
A cewar wani mazaunin unguwar mai suna Malam Misbahu Magaji sun dauki tsawon lokaci suna fuskantar wannan matsala da bunsuru kafin suN yanke shawarar kai karar bunsurun ga hukumar Hisba don daukar matakin da ya dace.
Shi ma wani mazunin unguwar Muttaka dahiru ya ce bunsuru yana da wani abin al’ajabi, saboda idan ka yi masa magana yana fahimta har ya aikata abin da ka gaya masa, “Misali idan ka ce ya je ya zauna a wuri kaza, haka zai tafi ya zauna. Idan ka kira shi ya karbi abinci duk zai bi umarninka yadda ka gaya masa,” inji shi.
Mataimakin Kwamandan Hisba na karamar hukumar Malam Abubakar Mati Salihu ya ce yanzu haka bunsuru yana hannunsu, kuma sun bayar da cigiyar mai bunsurun kuma da zarar sun same shi za su gurfanar da su gaban kotu. “Idan ba mu samu mai bunsurun ba, za mu kai shi hedikwatar Hukumar Hisba ta Jiha don daukar matakin da ya dace a kan bunsurun,” inji shi.