Za a gurfanar da ‘yan Boko Haram gaban kotu a Chadi
A ranar Litinin da ta gabata ne mahukunta a qasar Chadi suka ce za su gurfanar da waxansu mutane 10 waxanda ake zargin ‘yan Boko Haram ne a gaban kotu a N’Djamena, babban birnin qasar.Kamfanin dillanci labarai na AFP ya ruwaito cewar, ana zargin mutanen ne da shirya hare-haren bama-baman da suka yi sanadiyar mutuwar […]
A ranar Litinin da ta gabata ne mahukunta a qasar Chadi suka ce za su gurfanar da waxansu mutane 10 waxanda ake zargin ‘yan Boko Haram ne a gaban kotu a N’Djamena, babban birnin qasar.
Kamfanin dillanci labarai na AFP ya ruwaito cewar, ana zargin mutanen ne da shirya hare-haren bama-baman da suka yi sanadiyar mutuwar mutane 38 a qasar.
A farkon makon nan ne aka mayar da shari’ar kotun hukunta masu manyan laifuffuka ta Chadi, amma har yanzu ba a sanya ranar fara sauraron qarar ba.
Wannan shari’a ta masu tayar da kayar baya masu cibiya a Najeriya, ita ce irin ta ta farko da za a gudanar a qasar Chadi.
A cewar mahukuntan qasar, a cikin waxanda ake tuhumar akwai Mahamat Mustapha, wanda aka fi sani da Bana Fanaye, mutumin da ake zargi da hannu wajen kitsa harin, wanda aka kai a kan wata makaranta da kuma ofishin ‘yan sanda a N’Djamena ranar 15 ga watan Yuni.
Hakazalika, ana tuhumar Bana Fanaye da samar da makamai da kuma shigar da mutane cikin kungiyar ta Boko Haram.
Qasar Chadi dai tana fama da hare-haren qungiyar Boko Haram, kuma tana cikin qasashen da suke yaqi da qungiyar bayan qasashen Nijar da Kamaru.