Za a habaka kiwo da kasuwancin zuma a Najeriya
A tsakiyar wannan makon ne masu kiwon zuma a Najeriya suka gudanar da wani taro a Legas, birnin kasuwanci na Najeriya don share fagen taron masu ruwa-da-tsaki kan kiwon zuma a Nahiyar Afirka wanda za a gudanar a Abuja a watan Satumba mai zuwa. Taron kamar yadda gidan rediyon BBC ya ruwaito, ya duba sababbin […]
A tsakiyar wannan makon ne masu kiwon zuma a Najeriya suka gudanar da wani taro a Legas, birnin kasuwanci na Najeriya don share fagen taron masu ruwa-da-tsaki kan kiwon zuma a Nahiyar Afirka wanda za a gudanar a Abuja a watan Satumba mai zuwa. Taron kamar yadda gidan rediyon BBC ya ruwaito, ya duba sababbin hanyoyi kiwon zuma, da hanyoyin da za a bunkasa su don fitarwa zuwa kasashen ketare.
daya daga cikin manufofin taron shi ne yaki da masu sayar da zumar da aka yi wa algushu. Malam Ya’u Sarkin Baki, shi ne Shugaban kungiyar Masu Kiwon Zuma ta Arewa maso Yamma, ya ce babbar matsalar da suke fuskanta a kiwon zuma ita ce rashin kayan aiki.
Sannan akwai rashin shigar gwamnati cikin lamarin don bunkasa kiwon zuma ta hanyar samar da wadatattun kayan aikin da suke bukata. “‘Wata matsalar da muke fuskanta ita ce ta masu sayar da bara-gurbin zuma, kuma hanyar da za mu magance matsalar ita ce ta bai wa mutane horo a kuma ba su kayan aiki kuma ya kasance a kowace jiha ta Najeriya muna da manoman zuma 1,000 ta hakan ne za sa mu magance matsalar,” inji Malam Ya’u.
Ya kara da cewa: “Wani abu da zai bayar da mamaki shi ne kudajen zumar da ake da su a kasashen Turai sun gudu, kuma kasashen Afirka suka kwararo. Bincike ya nuna kusan kashi 48 cikin 100 suna Najeriya, to ka ga idan ba a dauki matakin kara fadada noman don ya bunkasa ba, to babu wata riba da za a samu a ciki.’’