Za a hana auren wuri ga ’ya’ya mata a Jigawa

Gwamnatin Jihar Jigawa da Qungiyar ‘Safe the Children’ na neman fito da wani tsari da zai tilasta wa iyaye su daina aurar da ’ya’yansu mata sai sun kai shekara 18. Wannan ya fito fili ne a wajen wani taro da aka gudanar a jihar, inda suka ce auren wuri yana sa ’ya’ya mata cikin matsalar […]

Za a hana auren wuri ga ’ya’ya mata a Jigawa

Gwamnatin Jihar Jigawa da Qungiyar ‘Safe the Children’ na neman fito da wani tsari da zai tilasta wa iyaye su daina aurar da ’ya’yansu mata sai sun kai shekara 18. Wannan ya fito fili ne a wajen wani taro da aka gudanar a jihar, inda suka ce auren wuri yana sa ’ya’ya mata cikin matsalar rayuwa lokacin haihuwa da zamantakewa saboda quruciya.

Sai dai nan take malaman addini da suka halarci taron suka soki tsarin, inda suka ce ana son yin amfani ne da damar wajen yi wa Musulunci zagon qasa. 

Da yake gabatar da qasida a wurin taron, wani likita mai suna Abbas Muhammed da ke aiki da Asibitin Shekoni ya ce aurar da yara mata kafin su kai shekara 18 a duniya yana cutar da yara mata, ya ce sukan fuskanci matsalolin rayuwa da cututtuka lokacin da suka dauki ciki ko wajen haihuwa saboda rashin kulawar mazan da suke aurensu. Ya ce lamari ya fi yawa a Arewa inda ake aurar da yara kimanin dubu 35 duk shekara, kuma da yawa yara matan da ake aurarwa ana hada su aure ne da tsofaffi abokan iyayensu ko kakaninsu. Ya ce, irin wadannan maza ba sa kula da lafiyarsu da kare haqqinsu na aure yadda ake buqata, inda ya ce sau da yawa wadansu matan saboda talaucin mazan sukan rasa ransu a lokacin haihuwa. 

“Yayin da matasa sukan auri yara mata amma ba su da sana’ar kirki, lamarinkan sa yaran su fada cikin wani hali saboda ba su iya dogaro da kansu, balle su kula da iyalinsu, don haka akwai buqatar a riqa barin yara maza da mata suna kammala karatu kafin a yi musu auren fari,” inji shi.

Wani jigo a Majalisar Malamai ta Jihar, Malam Yusha’u Dutse ya ce bata lokaci ake yi a ce za a tilasta iyaye su daina yi wa yara aure sai bayan sun kammala sakandare. Ya ce hakan ba daidai ba ne domin ya ci karo da tsarin shari’a. Ya ce ko ba doka iyaye da dama ba sa yi wa ’ya’yansu aure sai sun kammala sakandare don haka babu dalilin tilasta haka.

Babban Sakataren Ma’aikatar Mata ta Jihar, Alhaji Nasoro Gumel da suka dauki nauyin taron, ya ce Gwamnatin Tarayya ce ta bullo da shirin kuma ba a jihar ce kawai ba za a yi wannan shiri na hana iyaye aurar da ’ya’ya mata kafin su kai shekara 18. Ya ce lamari ne da ya hade qasashen Afirka baki daya, kuma an bullo da shi ne da nufin daqile yi wa yara auren wuri. Ya ce za su yi amfani da malamai wajen fadakar da iyaye muhinmancin jinkirtawa kafin a yi wa yara qanana aure.

Limamin Masallacin 744, Malam Yunus Muhammad ya shawarci iyaye su mayar da hankali wajen sanya ’ya’yansu a makaranta domin neman ilimi saboda hakan zai taimaka wajen inganta tarbiyyar ’ya’ya mata.  Kuma ya hori wadanda suka shirya bitar su daina wahalar da kansu domin Musulunci ya tsara wa Musulmi yadda za su gudanar da rayuwarsu a cikin sauqi.