Za a hana sanya nikabi a Senegal

A shekaranjiya Laraba ne Ministan Harkokin Cikin Gidan kasar Senegal Abdoulaye Daouda ya ce kasarsa tana shirin haramta wa mata sanya nikabi a bainar jama’a a wani yunkurin da take yi na hana kai hare-haren ta’addanci.Ministan ya kara da cewa bai kamata a kalli lamarin a matsayin “nuna kiyayya ga Musulmi ba”, saboda Senegal kasa […]

Za a hana sanya nikabi a Senegal
Za a hana sanya nikabi a Senegal

A shekaranjiya Laraba ne Ministan Harkokin Cikin Gidan kasar Senegal Abdoulaye Daouda ya ce kasarsa tana shirin haramta wa mata sanya nikabi a bainar jama’a a wani yunkurin da take yi na hana kai hare-haren ta’addanci.
Ministan ya kara da cewa bai kamata a kalli lamarin a matsayin “nuna kiyayya ga Musulmi ba”, saboda Senegal kasa ce da Musulmi suka fi rinjaye.
Idan wannan ya tabbata, kasar za ta kasance kasa ta biyar da ta haramta sanya nikabi a nahiyar Afirka.
kasashen Afirka da suka fara daukar irin wannan matakin su ne: Chadi da Gabon da Kongo-Brazzabille, inda ita ma Jamhuriyar Kamaru ta yi hakan a yankin Arewa-mai-Nisa a watan Yulin da ya wuce.
A makon jiya ne Shugaban kasar Macky Sall, wanda shi ma Musulmi ne, ya yi kira da a dauki kwararan matakai na yaki da ’yan ta’adda a kasar.
Har ila yau, a wani mataki na inganta tsaro gwamnatin kasar ta sanar da cewa za ta rufe layukan wayoyi da ba a yi musu rijista ba zuwa karshen watan nan.