Za a hana talakawa mallakar mota a Dubai
Hukumomi a masarautar Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa (United Arab Emirate -UAE), na shirin hana talakawa, masu karamin karfi hawan mota, don shawo kan cunkoson ababen hawa.Jaridar The National, ta ruwaito cewa, birnin Dubai yana cikin biranen duniya mafi bunkasa, amma duk da tituna masu fadin daukar jerin motoci shida a jere, cunkoson ababen […]
Hukumomi a masarautar Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa (United Arab Emirate -UAE), na shirin hana talakawa, masu karamin karfi hawan mota, don shawo kan cunkoson ababen hawa.
Jaridar The National, ta ruwaito cewa, birnin Dubai yana cikin biranen duniya mafi bunkasa, amma duk da tituna masu fadin daukar jerin motoci shida a jere, cunkoson ababen hawa ya addabi birnin. “Duk da cewa manyan biranen duniya na amfani da dabarun shawo kan cunkoso, wadanda suka hada da kara fadin hanyoyi da biyan haraji a kan ababen hawan da ke kai-kawo a tsakiyar birni da cin manyan motoci tara, daukacin wadannan ba sa cikin tsarin Dubai,” a cewar Hussain Lootah, Babban Daraktan kula da birnin.
Hussain Lootah, a wajen wani taron kara wa juna sani da aka gudanar a Jamus, ya bayyana wa jaridar cewa, masarautar na shirin hana masu karamin karfi mallakar motoci.
Jaridar The National, ta ruwaito cewa, “Za a yi la’akari da kimar albashin mutum, inda za a tantance ko ya cancanci mallakar mota.” Loota ya ce: “Kowa na da irin kayan alatun da rayuwarsa ke sha’awa, amma karfi da nagartar hanyoyinmu ba za su iya daukar wadannan motoci ba, ba tare da an yi dokar mallakar motocin ba.”
Mun san cewa takaita manufarmu a kan kimar albashi ba lallai ne ta yi cikakken tasiri ba, dopn haka za mu kara kudin ajiye ababen hawa da kudin man fetur da kudin sgiga kofa da kudin inshore da tarar cunkosobn ababen hawa, “ta yadda za mu karya kwarin gwiwar mutane wajen mallakar motoci,” kamar yadda aka ruwaito daga Daraktan kula da birnin.
Kafin a aiwatar da wannan doka, Gwamnatin Dubai za ta samar da motocin safara da jiragen kasa. A wannan makon za a fara gwada dokar, ta yadda za a takaita zirga-zirgar mutane a kan tituna.
Kimanin mutum dubu biyu da 97 suka bayyana ra’ayinsu game da wannan doka, inda mafi yawansu suka soki lamirin dokar, har ma wani na cewa, wannan ko dai irin tsokacin nan na “labaran barkwanci.”