Za a haramta amfani da bindiga a Papua New Guinea
A farkon makon nan ne gwamnatin kasar Papua New Guinea ta sanar da aniyyarta ta haramta amfani da bindigogi a duk fadin kasar, kamar yadda kafar yada labrai ta The Post Courier ta bayyana.Firaministan kasar Peter O’Neill ya ce mahukunta suna duba yiwuwar kafa dokar haramta amfani da kowane irin makami, inda ya ce matakin […]
A farkon makon nan ne gwamnatin kasar Papua New Guinea ta sanar da aniyyarta ta haramta amfani da bindigogi a duk fadin kasar, kamar yadda kafar yada labrai ta The Post Courier ta bayyana.
Firaministan kasar Peter O’Neill ya ce mahukunta suna duba yiwuwar kafa dokar haramta amfani da kowane irin makami, inda ya ce matakin zai shafi fararen hula da kuma ’yan sanda. “Ba ka bukatar rike wani makami kafin tabbatar da doka da oda a kasa. Abin da kake bukata shi ne daraja al’umma da ’yan sanda da kuma mata,” inji shi.
kasar wadda take a yankin Pacific ta fuskanci karuwar tada zaune tsaye a ’yan shekarun nan. Amma wasu suna ganin karbe bindigogi daga hannun mutane da wani jan aiki.
Akwai dubban bindigogi da suka bace a hannun ’yan sanda da kuma sojojin kasar, kodayake, an ce sace su aka yi, amma wani bincike da a gudanar a shekarar 2005 ya tabbatar da cewa an sayar da su ne ga kungiyoyin ’yan daba. Har ila yau, akwai wadanda suka fada hannun kabilu masu yaki da juna a yankunan karkarar kasar.