Za a hukunta direban Ministan da ya rasu

Duk da rahotanni na nuna cewa direban marigayi Minista a Ma’aikatar kwadago da Samar da Aikin yi, Mista James Ocholi, wato Taiwo James Elegbede ya rasu a Asibitin kasa da ke Abuja, akwai yiwuwar Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da gawarsa a gaban kotu domin hukunta shi.Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Dabid Lawal ne ya bayyana haka […]

Za a hukunta direban Ministan da ya rasu
Za a hukunta direban Ministan da ya rasu

Duk da rahotanni na nuna cewa direban marigayi Minista a Ma’aikatar kwadago da Samar da Aikin yi, Mista James Ocholi, wato Taiwo James Elegbede ya rasu a Asibitin kasa da ke Abuja, akwai yiwuwar Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da gawarsa a gaban kotu domin hukunta shi.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Dabid Lawal ne ya bayyana haka lokacin da yake wa manema labarai na Fadar Shugaban kasa bayani a shekaranjiya Laraba bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta kasa.
Babachir Lawal ya ce gwamnatin za ta yanke shawara kan ko a gurfanar da direban a gaban kotu ko a’a bayan rahoto na karshe kan binciken da ake yi ya zo mata.
Game da rahoton da kafafen watsa labarai suka bayar cewa iyalan Ocholi suna zargin akwai munakisa kan hadarin da ya ci Ministan Babachir ya ce: “Ba mu da wannan labari, kuma duk wanda yake wani rahoto sabanin cewa (Ocholi da matarsa da dansa) ba su mutu a hadari ba yana da damar da zai kain rahoto ga hukumomin tsaro kuma za su dauki mataki a kai.”
Hukumar Kiyaye Hadari ta kasa (FRSC) ta shaida wa Majalisar Zartarwar cewa bincikenta ya nuna Taiwo James Elegbede da ke tuka marigayi Minista Ocholi ba ya da lasisi.
Shugaban Hukumar FRSC, Boboye Oyeyemi da ya mika rahoton farko kan bincike game da hadarin da ya hallaka Minsitan da matarsa da dansa a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Lahadin da ta gabata ne ya bayyana haka.
Oyeyemi ya ce babu wata shaida da ke nuna diraben yana da lasisi a cikin taskar adana bayanan lasisi na kasa na hukumar.
“Bayanan da aka tattara sun nuna direban yana gudun wuce iyaka lokacin da tayar motarsu ta fashe. Motar da ta yi hadarin direbanta yana mugun gudu kuma sai ya taka birki da karfi. Wadannan dalilai biyu sun taimaka direban ya kasa shawo kan motar lokacin da tayar baya ta fashe,” inji Oyeyemi.
Ya ce sun samu alamun da suka nuna takun birki na tsawon mita 15 da mita 9.3 na motar, kirar Ledus Ld570 kafin ta fara wuntsilawa, kuma watso Ministan da dansa waje ya nuna mummunan gudun da motar take.
Ya ce watso Ministan da dansa da suke zaune a baya da motar ta ti ya tabbatar da cewa “ba a yi amfani da bel din daure jiki ba,” inji shi.
Sai Shugaban na FRSC ya ce dukkan motocin hukumomi da ma’aikatun gwamnati ba a yi rajistarsu yadda ya kamata ba, kuma galibinsu ba su dace da hawa kan hanya ba.
Ya ce hukumar ta ba da shawarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci kamfe din bin dokokin tuki da kauce wa mummunan gudu da sauransu, inda za a fara da sanya na’urorin takaita gudun motoci a motocin ’yan kasuwa.
Sai hukumar ta bukaci wakilan majalisar da shugabannin hukumomi da ma’aikatun gwamnati su yi koyi da Shugaba Buhari wajen bin dokokin tuki.
Mista Babachir Lawal, ya ce Shugaba Buhari ya amince a hanzarta bayar da aiki ga ’ya’yan Ocholi biyu da suka kammala jami’a aiki a duk ma’aikata ko hukumar Gwamnatin Tarayya da suka zaba, yayin da sauran biyu da suke karatu za a a ba su tallafin karo ilimi har zuwa jami’a. Kuma Gwamnantin Tarayya za ta dauki nauyin duk kudin da za a kashe wajen bikin binne Ocholi da matarsa da kuma dansa.