Za a hukunta iyayen da suka bar ‘ya’yansu na bara a kan titi a Oyo

Gwamnatin Jihar Oyo ta ce wani bincike da ta gudanar ta gano cewa ana samun karuwar mabarata a kan hanyoyi ne dalilin sakacin iyaye wajen lura da tarbiyyar ’ya’ya musamman masu lalurar nakasa. Sannan matsalolin fyade ga ’yan mata da fataucin kananan yara suna da nasaba da rashin kular iyaye. Don haka  gwamnatin ta ce […]

Za a hukunta iyayen da suka bar ‘ya’yansu na bara a kan titi a Oyo

Mabarata mata da babu naqasa a jikinsu xauke da qananan yara a kan tsakiyar hanyar mota a Ibadan

Gwamnatin Jihar Oyo ta ce wani bincike da ta gudanar ta gano cewa ana samun karuwar mabarata a kan hanyoyi ne dalilin sakacin iyaye wajen lura da tarbiyyar ’ya’ya musamman masu lalurar nakasa. Sannan matsalolin fyade ga ’yan mata da fataucin kananan yara suna da nasaba da rashin kular iyaye.

Don haka  gwamnatin ta ce ta sha alwashin nan ba da dadewa ba za a yi adabo da wadannan matsaloli da zarar dokar hukunta iyaye masu sakaci da kula da ’ya’yansu ta fara aiki a jihar.

Kwamishinar Harkokin Mata da Walwalar Jama’a Hajiya Faosat Sanni ta bayyana haka lokacin da ta ziyarci makarantar makafi ta Ogbomoso da aka gina a 1968. Ta ce “Bai kamata iyaye su kyale ’ya’yansu masu dauke da wata nakasa suna yawon bara a kan hanyoyi ba domin nakasar jikin mutum ba ta zama makami ko hanyar yawon bara ba. Kamata ya yi a rika aikewa da irin wadannan yara zuwa makarantun horar da nakasassu ta yadda za su amfani rayuwarsu kasa ta amfana da su kamar sauran mutane.”

Kwamishinar ta nuna farin ciki da jin dadin kan yadda daliban makarantar makafin suka jajerice wajen koyon sana’o’in hannu da suke yin amfani da su wajen dogaro da kai ba tare da bata rayuwarsu ta hanyar rokon mutane a kan hanyoyi ba.

Binciken da Aminiya ta gudanar ta gano cewa, a Jihar Oyo babu kananan yara masu yawon bara a cikin gidaje da shagunan sayar da abinci kamar yadda ake samun yara almajiran makarantar allo a Arewa. Sai dai akwai nau’in mabarata  nakasassu kamar makafi da guragu da kutare da mafi yawancinsu ’yan Arewa ne da mahukunta suka killace su a wani sansani da jama’a suke zuwa suna kai masu sadakar kudi da tufafi da kayan abinci.

Binciken ya gano cewa kashi 80 cikin 100 na masu yawon bara a Kudu maso Yamma sun fito ne daga Arewa da kasar Nijar wadanda Gwamnatin Jihar Oyo ta ce nan bada dadewa ba za ta fara mayar da su zuwa garuruwansu na asali.