Za a hukunta iyayen da suka hana yara samun ilimi a Adamawa

Babban taron na da nufin tsara dabarun inganta fannin ilimi daidai da tsarin da gwamnatin jihar ta yi a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri.

Za a hukunta iyayen da suka hana yara samun ilimi a Adamawa

Gwamnatin Jihar Adamawa ta bayyana shirin gurfanar da duk iyayen da suka hana ’ya’yansu samun ilimi.

Kwamishinan ilimi da ci gaban jama’a na Jihar Adamawa, Dakta Umar Garba Pella ne ya bayyana hakan bayan wata ganawar sirri da ya yi da masu ruwa da tsaki a ɓangaren ilimi.

Taron wanda mataimakiyar Gwamnan Jihar, Farfesa Kaletapwa Farauta ta kira, ya gudana ne a ɗakin taro na ofishinta a ranar Talata.

Ya ce babban taron na da nufin tsara dabarun inganta fannin ilimi daidai da tsarin da gwamnatin jihar ta yi a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri.

Da take jawabi bayan taron, Dakta Pella ta jaddada ƙudirin gwamnatin jihar na magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta.

Ya bayyana cewa, an kafa kwamitin sa ido da tantancewa don tabbatar da ingantaccen sa ido don samun ilimi mai inganci a makarantu, yana mai jaddada cewa iyayen da ke hana ‘ya’yansu samun ilimi za su fuskanci hukuncin shari’a.

Dakta Pella, wanda shi ma ya gabatar da jawabin buɗe taron, ya nuna damuwarsa kan yadda ɓangaren ilimi ke gudanar da ayyukansa duk da ɗimbin jarin da aka zuba a harkar.

Ya yi kira da a samar da ingantaccen haɗin kai da kuma bada himma wajen cimma nasarar da ake buƙata a harkar.

Ya kuma yaba wa Gwamna Fintiri a matsayin shugaba mai bin diddigin sakamakon ayyukansa tare da jaddada buƙatar dukkan masu ruwa da tsaki su haɗa kai don inganta harkar ilimi.

Taron ya samu halartar manyan jami’an ilimi da suka haɗa da babban sakatare, daraktoci da shuwagabannin Ƙungiyar malamai ta Najeriya NUT, da wakilai daga hukumar kula da makarantun gaba da firamare, sakatarorin ilimi da ƙaddamar da shugabanni daga Ƙananan hukumomi 21 a jihar.