‘Za a hukunta ma’aikatan da ke wasa da aiki a yankunan Maiyama da Koko-Besse’

Shugabannin kananan hukumomin Maiyama da Koko-Besse a Jihar Kebbi, Alhaji Buhari Aliyu Koko da Alhaji Umaru Salla Sambawa U.U., sun ce duk ma’aikacin da bai zuwa wurin aiki a kan lokaci zai dandana kudarsa. Shugabannin sun bayyana haka ne a lokacin da suke zantawa da manema labarai a Ma’aikatar kananan Hukumomi ta Jihar da ke […]

‘Za a hukunta ma’aikatan da ke wasa da aiki a yankunan Maiyama da Koko-Besse’
‘Za a hukunta ma’aikatan da ke wasa da aiki a yankunan Maiyama da Koko-Besse’

Shugabannin kananan hukumomin Maiyama da Koko-Besse a Jihar Kebbi, Alhaji Buhari Aliyu Koko da Alhaji Umaru Salla Sambawa U.U., sun ce duk ma’aikacin da bai zuwa wurin aiki a kan lokaci zai dandana kudarsa. Shugabannin sun bayyana haka ne a lokacin da suke zantawa da manema labarai a Ma’aikatar kananan Hukumomi ta Jihar da ke Birnin Kebbi. Alhaji Buhari Aliyu Koko ya ce babu yadda za a yi a samu ci gaba face ma’aikaci yana zuwa wurin aiki a kan lokaci, kuma yana gudanar da aikin. Ya ce duk ma’aikacin da aka samu ba ya zuwa wurin aiki a kan lokaci, karamar hukuma za ta ladabtar da shi. Shi kuwa Alhaji Umar Sambawa cewa ya yi ma’aikaci ba ya da wani dalili na rashin zuwa wurin aiki domin kuwa dukkan bukatun ma’aikatan gwamnati ta biya musu, domin haka bai kamata ma’aikata na karbar albashinsu a cikin lokaci ba, su kuma ba su zuwa wurin aikinsu cikin lokaci. Aminiya ta tuntubi shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta Jihar Kebbi Alhaji Musa Ibrahim dan’illela inda ya shawarci ma’aikatan kananan hukumomin jihar su kasance masu tsoron Allah, ya ce duk ma’aikacin da aka kara masa albashi kuma ana biyansa a kan kari in har ba ya zuwa wurin aiki a kan lokaci, to ya cuci kansa, duk kudin da aka biya shi ya ci amana zai mayar da su gobe kiyama.