Za a hukunta mutum 19 wadanda ake zargi da kisan Janar Alkali
Rundunar ‘yan sandan a jihar Filato, ta ce ta kama wasu mutum 19 da ake zargi da hannu a kisan Manjo Janar Alkali mai ritaya. Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar DSP Tyopev Matthias Terna ya bayyana wa manema labarai cewa, za a mika wadanda ake zargin da kisan marigayin a Kotu […]
Rundunar ‘yan sandan a jihar Filato, ta ce ta kama wasu mutum 19 da ake zargi da hannu a kisan Manjo Janar Alkali mai ritaya.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar DSP Tyopev Matthias Terna ya bayyana wa manema labarai cewa, za a mika wadanda ake zargin da kisan marigayin a Kotu don yanke masu hukunci.