Za a iya daure masu karya dokar hana acaba shekara 3 – Gwamnatin Legas
Gwamnatin Jihar Legas a ranar Laraba ta ce, wadanda suka karya dokar hana acabar da ta kafa a jihar za su iya fuskantar hukuncin daurin shekara uku a gidan yari. Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran fara aiwatar da dokar a mataki na biyu ranar Juma’a. Rikicin ’Yan Acaba Da […]
Gwamnatin Jihar Legas a ranar Laraba ta ce, wadanda suka karya dokar hana acabar da ta kafa a jihar za su iya fuskantar hukuncin daurin shekara uku a gidan yari.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran fara aiwatar da dokar a mataki na biyu ranar Juma’a.
- Rikicin ’Yan Acaba Da ’Yan Sanda Ya Janyo Asarar Rai A Legas
- Sannu a hankali Najeriya na komawa mulkin kama-karya – Jonathan
- An sake sa dokar hana acaba a kananan hukumomin Legas 4
Kwamishinan Sufuri na jihar, Dokta Frederic Oladeinde, ne ya bayyana haka a lokacin wani taron manema labarai a Ikeja.
Ya kuma ce dokar hana acaba a mataki na biyu ta kasance a kananan hukumomi 10 ne na jihar.
A watan Agustan da ya gabata ne gwamnatin jihar ta ayyana saka dokar haramta acaba a wasu kananan hukumomi hudu, kari a kan guda shidan da ta hana a baya.
Sabbin kananan hukumomin sun hada da Kosofe (Ikosi-Isheri da Agboyi-Ketu); Mushin (Odi-Olowo); Oshodi (Oshodi-Isolo da Ejigbo) da kuma Shomolu (Bariga).
Kwamishinan ya kuma ce, “Muna kira ga jama’a da su yi biyayya ga dokar. Daga direbobi da fasinja duk suna iya fuskantar daurin shekara uku a gidan yari idan an gurfanar da su a gaban kuliya.
“Za a rike baburansu tare da ragargaje su a idon jama’a, daidai da tanadin sashe na 46, karamin sashe na 1, 2 & 3 na dokar kawo sauyi a bangaren sufuri (TSRL) ta jihar Legas ta shekarar 2018.
“Muna kira ga jama’a da su hada kai da gwamnatin jihar ta hanyar bin shawarar da aka tanada na yakar haramta acaba, domin kwanciyar hankali ya dawo jiharmu,” inji Mista Oladeinde.
Ya ce, jami’an Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Legas, LASTMA 200 ne aka tura su shiga cikin sauran hukumomin tsaro domin aiwatar da dokar a unguwanni.
A cewarsa, tsawaita dokar zuwa wasu kananan hukumomi hudu da unguwanni na kan hanyar da ta dace don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.