Za a iya gamawa da Boko Haram cikin wata uku – Janar IsaZa a iya gamawa da Boko Haram cikin wata uku – Janar Isa
Tsohon Kwamandan Kwalejin Horar da Manyan Hafsoshin Soja da ke Jaji a Jihar Kaduna, Manjo Janar Muhammadu danhanne Isa (mai ritaya) ya ce za a iya ganin bayan ’yan Boko Haram a cikin lokacin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nema.Manjo Janar M.D. Isa ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu, inda […]
Tsohon Kwamandan Kwalejin Horar da Manyan Hafsoshin Soja da ke Jaji a Jihar Kaduna, Manjo Janar Muhammadu danhanne Isa (mai ritaya) ya ce za a iya ganin bayan ’yan Boko Haram a cikin lokacin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nema.
Manjo Janar M.D. Isa ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu, inda ya ce a yanzu haka an ci kashi 30 na yakin da ake yi da ’yan Boko Haram ta hanyar yaki da cin hanci da rashawa da kuma ziyarar da Buhari ya kai kasashen Nijar da Chadi da Kamaru da Benin.
Janar Isa ya ce ’yan Boko Haram ba cikakkun ’yan tawaye ba ne saboda ba su da goyon bayan jama’a, kuma ’yan Najeriya da kasashen duniya suna goyon bayan abin da Shugaba Buhari yake yi.
“Na san za a cimma nasara cikin wata uku ka kafin wata uku domin na san shugaban sojojin Najeriya Laftana Janar Tukur Burutai da Mashawarcin Shugaban kasa kan Tsaro Manjo Janar Muhammadu Monguno (mai ritaya) da Shugaban Sojin Sama Iya Mashal Saddikue Abubakar, ba su da wasa, in sun sa abu a gaba sai sun ga bayansa,” inji shi.
Janar Isa ya ce zuwan hafsan sojojin Maiduguri ya dauki lokaci tare da su ya kara musu kwarin gwiwa. “Ziyarar da Janar Buratai ya kai bayan kwanaki da nada shi inda ya yi Sallah da sojojin da ke filin daga a Jihar Yobe, kuma ya ba su hakkokinsu ya karfafa gwiwar sojojin matuka. Wani Kanar ya yi min waya cewa ya ga abin mamaki inda maimakon a ba shi kashi goma na alawus dinsa a ba shi sauran in ya dawo, an ba shi kudinsa a dunkule. Kuma ya ce haka aka yi daga kurtun soja har zuwa Janar.”
Ya ce shugaban sojin sama kuma ya je Kaduna ya saurari sojoji kanana da manya inda abin ya burge kowa. “Don haka lokaci ya yi da ’yan Boko Haram za su yi saranda,” inji Janar Isa.
Ya nuna damuwa kan yadda ’yan Boko Haram ke amfani da yara wajen kai harin kunar bakin wake, inda ya ce tun da masu kai harin na cikin jama’a ne, ya kamata jama’a rika taimakawa da kai rahoton wanda ba su amince da take-takensa ba ga hukumomi.